An dauki matakin rigakafin cutar Lassa a Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta samar da cibiyoyin killace wadanda ka iya kamuwa da annobar cutar zazzabin Lassa domin jiran ko-ta-kwana. A cewar Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Babatunde Ipaye, an samar da cibiyoyin ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke garin Shagamu da asibitin gwamnatin jihar da ke unguwar Ijaye da babban […]

An dauki matakin rigakafin cutar Lassa a Ogun
An dauki matakin rigakafin cutar Lassa a Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta samar da cibiyoyin killace wadanda ka iya kamuwa da annobar cutar zazzabin Lassa domin jiran ko-ta-kwana.

A cewar Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Babatunde Ipaye, an samar da cibiyoyin ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke garin Shagamu da asibitin gwamnatin jihar da ke unguwar Ijaye da babban asibitin Gwamnatin Tarraya da ke unguwar Iberekodo, dukanninsu a Abekuta. Ya ce an dauki matakin ne domin jiran ko-ta-kwana, domin a halin da ake ciki a yanzu babu labarin bullar cutar a fadin jihar, sai dai duk da haka ya bayyana aniyar gwamnatin na wayar wa al’ummar jihar kai bisa cutar zazzabin na Lassa; domin yin rigakafinta. A kan haka ya yi kira ga jama’ar jihar da su rungumi akidar tsaftace jikinsu da muhallinsu, domin samun kariya daga cutar, wadda baraye ke yadawa.
Kwamishinan ya kara da cewa, akwai labarin bullar cutar ta zazzabin Lassa a wasu jihohi masu makwabtaka da Jihar Ogun, inda mutum uku suka kamu a Jihar Ondo; an kuma samu labarin bullar cutar a wani yankin Jihar Legas da ke kusa da garin Sango Ota. Don haka ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da yin taka-tsan-tsan, ya kuma ba da lambobin wayar da za a iya tuntuba da zarar an ga alamun bullar cutar.
Ya bayyana cewa ma’aikatar lafiya za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da ma’aikatar ilimi ta jihar, domin yin amfani da makarantu a wajen wayar wa al’ummar kai bisa cutar zazzabin Lassa, domin a cewarsa idan malamai suka ilimantar da dalibansu game da cutar, za su sanar da iyayensu da sauran jama’ar gari.
A Jihar Legas mai makwabtaka da Ogun, Kwamishinan Lafiya a jihar, Dokta Jide Idris ya bayyana cewa a yanzu mutum 92 aka killace bisa harbuwa da kwayar cutar zazzabin Lassa a jihar, inda ya ce an samu bullar cutar ne a jihar bayan da wani dalibin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya dawo gida duba mahaifiyarsa, sai ya kwanta ciwo; inda aka kwantar da shi asibitin Ahmadiyya da ke a Ojokoro.
Gwamnatocin jihohin sun bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu, domin gwamnati na yin duk abin da ya dace don shawo kan annobar cutar.