An Dauki Sabbin Malamai Guda 5,000 A Jigawa

Rahotanni daga Jigawa na cewa Gwamna Umar Namadi ya dauki malamai 3,143 aikin dindindin da wasu 2,445 na wucin gadi. Gwamna Namadi da yake jawabi a wajen bikin rabon takardun daukar aikin a filin taro na Malam Aminu Kano Triangle Dutse, ya ce, samar da ayyukan yi na daga cikin ajandarsa guda 12 da ya […]

An Dauki Sabbin Malamai Guda 5,000 A Jigawa

Rahotanni daga Jigawa na cewa Gwamna Umar Namadi ya dauki malamai 3,143 aikin dindindin da wasu 2,445 na wucin gadi.

Gwamna Namadi da yake jawabi a wajen bikin rabon takardun daukar aikin a filin taro na Malam Aminu Kano Triangle Dutse, ya ce, samar da ayyukan yi na daga cikin ajandarsa guda 12 da ya shirya wa jihar.

Ya bayyana cewa, babu wata manufar gwamnati da za a iya aiwatarwa ba tare da isassun ma’aikata masu inganci ba.

“Ajandarmu guda 12 na daukaka Jihar Jigawa sun hada da samar da ilimi mai inganci ga daukacin yaran jihar nan.

“Domin samun nasarar haka, dole ne mu inganta malamanmu, shi ya sa muka dauki malaman da suka kai wannan adadin aiki.

“Za mu ci gaba da yin hakan har sai mun samu wadatattun malami a kowane aji,” in ji Gwmna Namadi.

Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, ya ce malaman da suka yi aikin koyarwa na wucin gadi na tsawon shekaru biyu a jihar ne aka mayar na dindindin, masu fansho da duk wani abu da ma’aikaci ke samu bayan sun ci jarrabawa.

“Duk malamai 3,143 da aka dauka aiki an dauke su ne bisa cancanta, kuma an tabbatar mana da cewa suna da kwarewa kuma za su ba yaranmu ingantaccen ilimi.”

Ya shaida wa sabbin ma’aikatan da aka dauka cewa, hukumar za ta ci gaba da sanya ido a kansu, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen korar duk wanda ya ki bin ka’idojin daukar ma’aikata.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta