An dauki zomo aikin dan sanda a Amurka
Carson ta gano zomon yana da “saukin kai da haba-haba da mutane.
A wani abu mai kama da fim din nan na “Zootopia” da aka yi a shekarar 2016, ’yan sandan birnin Kalifoniya a kasar Amurka sun dauki wani zomo aiki a rundunarsu.
“Muna farin cikin gabatar da jami’in sanya walwala da karfafa gwiwa, Percy,” in ji Sashin ’Yan sanda na Birnin Yuba a wata sanarwa a shafinsa na Facebook a ranar 5 ga Afrilun nan.
- ’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 2, sun raunata da dama a Katsina
- Karashen Zabe: INEC ta raba kayan aikin zabe a Adamawa
A cikin sanarwar sashin ya bayyana cewa, “YCPD yana da tsarin sanya walwala ga dukkan ma’aikata da iyalansu.”
Tsarin “Yana karfafa muhimmancin ba da fiffiko kan lafiyar jiki da kwakwalwa da samar da kayayyaki da albarkatun rage gajiya tare da samar da ginshiki mai inganci ga jin dadin rayuwa.”
Sabon aikin da aka ba ofisa zomo Percy shi ne “Kwanciya ko zama ko tsayuwa ko kishingida a sashin ’yan sandan a yini kuma shi dabba ne da zai taimaki kowa,” in ji sanarwar.
Sashin ya sa hotunan Percy sanye da rigar aiki mai suna “Police K9” irin wadda ’yan sanda karnuka ke sanyawa.
Dan sanda zomo Percy mai launin ruwan kasa da fari wata ’yar sandan Birnin Yuba mai suna Ashley Carson ce ta tsince shi ne a ranar 21 ga Oktoban 2022, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Carson ta gano zomon yana da “saukin kai da haba-haba da mutane,” in ji sanarwar.
An dauki zomon zuwa sashin kula da dabbobi amma ba a gano mamallakansa ba.
Sai masu Nazarin Ayyukan na ’Yan sandanmu suka zabi rike shi,” in ji sashin a sanarwar.
An sa wa zomon sunan “Percy” ne, saboda an tsince shi ne a Titin Percy – kuma yana ci gaba da rayuwa tare da ’yan sandan yankin tun wancan lokaci.
’Yan sanda da dama suna jin dadin zama da shi, yayin da wasu suke kokarin yadda za su saba da zomo ya zauna a cikin ’yan sanda,” sanarwar Facebook din ta bayyana.
Kafar labarai ta Fox News Digital ta tuntubi ’Yan sandan Birnin Yuba don jin ta bakinsu kan wannan sabon dan sanda nasu.
Yayin da aka fi ganin karnuka suna aiki a sashin ’yan sanda akalla akan samu kyanwa daya a kowane sashi nasu.
A shekarar 2018, wani sashi na ’yan sandan Michigan ya ba da sanarwar “daukar hayar” wata kyanwa a matsayin ’yar sanda kamar yadda kafar labarai ta Fox News Digital ta bayar da rahoto.
Aikinta ya hada da “Sa ido kan jama’a da kula da sashi na K9 da kuma kwanciya a jikin ’yan sanda.”