An ɗaura auren Sadiya Haruna a karo na 10

Za a shafa Fatihar auren Sadiya Haruna da angonta Babagana Audu Grema a Maiduguri

An ɗaura auren Sadiya Haruna a karo na 10

A Juma’ar nan, 5 ga watan Yuli, 2024, jarumar TikTok, Sayyadda Sadiya Haruna, ta amarce a karo na 10.

A safiyar Juma’ar Sadiya Haruna ta dora katin gayyatar daurin auren nata, wanda zai gudana a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Auren Sayyada Haruna da angonta mai suna Hon. Babagana Audu Grema na zuwa ne ’yan watanni ƙalilan bayan kotu ta raba aurenta da tsohon mijinta, shahararren dan TikTok, G-Fresh Al-Amin.

Auren Sadiya Haruna da G-Fresh dai bai yi tsawon kwana ba, inda takaddama ta rika dabaibaye zaman nasu, har a karshe suka kare a gana kotun Musulunci.

Dambarwar auren Sadiya Haruna da G-Fresh ta karaɗe kafofin sada zumunta inda ake ta ce-ce-ku-ce a kai, kafin daga karshe kotun ta raba auren.

Mako guda ke nan da Sadiya Haruna ta yi wa G-Fresh wankin babban bargo a lokacin da aka karbi bakuncinta a shirin tattauna na Gabon’s Talk Show, na tauraruwar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon.

Sadiya ta shaida wa Gabon cewa aurenta takwas kafin ta zama matar G-Fresh.

Shi ma daga bisani ya tabbatar wa shirin na Hadiza Aliyu Gabon cewa shi ne na tara a jerin mazajen da Sayyadar ta aura.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Juma’ar ce kuma za a daura auren takwarar Sayyada, wato Sadiya Gyale a Jihar Kano.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa