An daura auren ’yan Saudiyya ta shafin bidiyon intanet na Skype
Wani dan kasar Saudiyya da ke Amurka ya auri matarsa da ke zaune a Saudiyyar ta hanyar shafin sadarwa d ahoton bidiyo na Skype, inda suka furta kalmomin amincewa su zama amta da miji, a gaban shehin Malami Fayez Fawaz Al Nafili, wanda ya jagoranci gudanar da auren, kamar yadda jaridar Okaz ta Saudiyya ta […]
Wani dan kasar Saudiyya da ke Amurka ya auri matarsa da ke zaune a Saudiyyar ta hanyar shafin sadarwa d ahoton bidiyo na Skype, inda suka furta kalmomin amincewa su zama amta da miji, a gaban shehin Malami Fayez Fawaz Al Nafili, wanda ya jagoranci gudanar da auren, kamar yadda jaridar Okaz ta Saudiyya ta ruwaito.
“Da farko na cika da mamaki, lokacin da aka bukaci in daura auren tsakanin mutumin da ke Amurka da matar da ke Saudiyya,. Don wannan shi ne karo na farko da na shafe shekara bakwai ina jagorancin harkokin addini, da aka taba bani babbar wayar hannu ta alfarma, don gudanar da wannan al’amari,” a cewar Fazyez Fawaz Al Nafili
Ayedh Al Nakool, angon da ke karatu a Amurka, ya nuna farin cikinsa kan yadda aka samu nasarar gudanar da auren. “Yanzu ina jiran dama ta samu in tafi Saudiyya don gudanar da sauran bukukuwan aurena, sannan in dauko matata mu tare a Amurka,” inji shi.
A Saudiyya an sha daura aure, ba tare da kasancewar daya daga cikin ma’auratan ba, tun zamanin da.