An daura auren zawarawa 100 a Kaduna

Ranar Lahadin da ta wuce ne aka daura wa zawarawa 100 a Kaduna a wani shiri na taimaka wa masu son yin aure amma ba su da hali. daurin auren shi ne karo na farko a jihar kuma kungiyar Darur Rahma ce ta shirya a Masallacin Juma’a na Al-Mannar da ke Unguwar Rimi, KadunaDaga cikin […]

An daura auren zawarawa 100 a Kaduna
An daura auren zawarawa 100 a Kaduna

Ranar Lahadin da ta wuce ne aka daura wa zawarawa 100 a Kaduna a wani shiri na taimaka wa masu son yin aure amma ba su da hali. daurin auren shi ne karo na farko a jihar kuma kungiyar Darur Rahma ce ta shirya a Masallacin Juma’a na Al-Mannar da ke Unguwar Rimi, Kaduna
Daga cikin manyan bakin da suka halarci dauren auren akwai Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero da Sheikh Aminu Daurawa daga Jihar Kano.
Babban Limamin Masallacin Sarkin Musulmi Bello, Sheikh Balele Wali ne ya jagoranci daurin auren tare da wasu malamai 10 da misalin karfe 1:00 na rana.
Sai dai wasu daga cikin abokan angwayen da suka halarci daurin auren sun koka kan yadda aka hana su shiga cikin masallaci domin yin Sallar Azahar tare da manyan baki saboda tsaro. Sai daga baya aka bar su suka shiga domin samun daurin auren.
A jawabinsa kafin fara daura auren, Sheikh Balele Wali ya roki Allah Ya sanya wa aurarrakin albarka tare da jan hankalin angwayen da amaren su ji tsoron Allah. “Muna kira ga ma’auratan su ji tsoron Allah su rike auren da muhimmanci. Daga yanzu hakkokin matan da ke kan iyayensu ya dawo kan mazajensu. Da fatan Allah Ya ba su ikon daukar wannan nauyi,” inji shi.
Shugaban Hisbah na Jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar Darur Rahmah Sheikh Is’hak Yunus Almadani ya ce akalla kowace amarya an kashe mata kusan Naira dubu 200. “Allah Ya taimaka mun cika alkawarin da muka dauka na shirya wannan aure. Muna kuma gode wa wadanda suka taimaka wajen tabbatuwar wannan abin alheri, musamman Gwamnan Jihar Kaduna wanda ya taimaka domin ganin abin ya tabbata.”
Ya ce “Akalla yanzu haka muna da kekunan dinki da na nika da za a ba kowace amarya. Muna kuma da gado da zannuwan gado da za a ba su baya ga kayan abinci. Duk wannan bayin Allah ne suka taimaka ciki har da matar Mataimakin Shugaban kasa, Hajiya Amina Namadi Sambo.”
Sheikh I’shak Yunus ya ce da farko da suka yanke shawarar shirya aurar da zawarawa a jihar wasu sun dauka da wasa ne, sai ga shi yanzu abin ya tabbata.”Yanzu haka mutanen da ke zuwa suna neman fom sai kara yawa suke a kullum. Saboda haka muna fata za su yi hakuri har sai nan gaba,” inji shi.
Ya ce Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ne ya dauki nauyin biyan kudin sadakin amaren daga aljihunsa.
Sheikh Aminu Daurawa wanda shi ne shugaban Hisbah na Jihar Kano kira ya yi ga gwamnatin Jihar Kaduna ta shiga cikin harkar tsundum kamar yadda takwararta ta Kano ta yi domin samun ingancin al’amarin.
Ya roki Gwamna Yero ya tabbatar nan gaba an hada auren tare da na Kiristoci “ Muna kuma kira ga ma’auratan su guji duka da zagin amarensu domin yin hakan ya saba wa karantarwar Musulunci,” inji shi.
Gwamna Yero ya ce da yardar Allah idan za a sake ba da auren nan gaba za a hada da Kiristoci domin karin hadin kai. Ya yaba wa kungiyar Darur Rahmah da ta fito da wannan tsari wanda ya ce zai taimaka wajen rage yawan aikata ba daidai ba a cikin al’umma.
Matar Mataimakin Shugaban kasa Hajiya Amina Namadi Sambo a jawabinta a dakin taro na ’Yar’aduwa da ke Dandalin Murtala Muhammad inda aka shirya wa angwaye da amare walima yaba wa wadanda suka hada Sunnar Manzon Allah ta yi.
“Aure Sunna ne na Manzon Allah kuma abu ne mai karfi, ina fatan angwaye da amaren za su yi aiki da nasihohi da aka yi masu, su kuma yi aiki da shawarwari da aka ba su, su zauna cikin lumana da junansu,” inji ta.