An daura wa nakasassu 104 aure a Saudiyya

An daura wa wadansu nakasassu guda 104 aure a wani babban otel da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya.Bikin wanda wata kungiyar agaji mai the Society for Physically Disabled Adults (Harakia) ta shirya, an gudanar da shi ne a ranar Lahadin da ta gabata. Hakazalika, bikin ya samu halartar Gimbiya Hussa bint Salman bin Abdul’aziz.Kodayake, […]

An daura wa nakasassu 104 aure a Saudiyya
An daura wa nakasassu 104 aure a Saudiyya

An daura wa wadansu nakasassu guda 104 aure a wani babban otel da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Bikin wanda wata kungiyar agaji mai the Society for Physically Disabled Adults (Harakia) ta shirya, an gudanar da shi ne a ranar Lahadin da ta gabata. Hakazalika, bikin ya samu halartar Gimbiya Hussa bint Salman bin Abdul’aziz.
Kodayake, wata jarida ta ruwaito cewa bikin an kayyade wadanda aka gayyata ne kawai ga masu hannu da shuni. Rahoton ya ce kusan shekara 40 ke nan a kasar idan za a yi biki ana gayyatar kowa da kowa ne. Kuma ana fara bikin ne da marece  zuwa tsakiyar dare. Amma a yanzu ana fara bikin ne da daddare kuma wadanda kawai aka bai wa katin gayyata ne za su iya shiga zauren taron.
Har ila yau, a cikin katin gayyatar ana bayyana cewa  irin suturar da mutum zai sanya da sauransu. A kan bayyana tsawon lokacin da za a kwashe da kuma lokacin da za a raba abinci ga baki.