An daure barayin shanu shekara biyu a Jigawa
Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse fadar Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Ibrahim Yusuf Harbo ta daure wasu makiyaya biyu masu suna Abubakar Yunusa da dan uwansa Abdulmumini, mazauna kauyen Baranda da ke karamar Hukumar Dutse, saboda samunsu da laifin satar wata saniya mallakar Suleiman Adamu mazaunin garin Baranda Wadanda ake tuhumar […]

Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse fadar Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Ibrahim Yusuf Harbo ta daure wasu makiyaya biyu masu suna Abubakar Yunusa da dan uwansa Abdulmumini, mazauna kauyen Baranda da ke karamar Hukumar Dutse, saboda samunsu da laifin satar wata saniya mallakar Suleiman Adamu mazaunin garin Baranda Wadanda ake tuhumar dukansu sun amsa laifinsu kuma sun yi ikirarin aikata satar, inda alkalin ya yi amfani da sashi na 140 da 142 da 146 da 147da 171 da sashi na 123 wajen yanke musu hukuncin daurin shekara biyu a gidan maza ba tare da zabin biyan tara ba.
Masu laifin sun shaida wa alkalin cewa sun saci saniyar ce suna shirin sayar da ita su kashe kudin ba don biyan wata bukata da ta dame su ba.
An yi wa saniyar kudi a gaban alkali kan Naira dubu 130.
Da yake hukuncin, alkalin ya ce laifin da barayin saniyar suka aikata ya saba wa sashi na 147 na kundin Final Kod.
Sun nemi alkalin kotun ya yi musu sassauci saboda wannan shi ne laifi na farko dasuka aikata.
dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun Sufeto Sani Garba ya amince da bukatar masu laifin na neman a yi musu sassauci kasancewar wannan ne karo na farko da suka taba gurfana a gaban kotu.
Sai dai alkalin ya yi watsi da bukatar, inda ya yanke musu hukuncin daurin shekara bibbiyu a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, ya ce a haka ma an yi musu sassauci ne domin za a iya hada musu da tara da bulala 30 kowannensu.
Kafin Sallar Layya mutanen yankin Baranda sun sha kaiwa-da-kawowa a zauren Majalisar Dokoki da ofishin Hakimin Dutse, Alhaji Jamilu Sunusi da ofishin ’yan sanda na karamar Hukumar Dutse domin isar da korafinsu a kan yawaitar sace-sacen shanu da wadansu miyagu suka saka su a gaba.
Yankin Baranda dai yanki ne da yake da dausayi kuma ya shahara wajen albarkatun noman rani da damina, inda kuma yake fama da sace-sascen shanu da sauran dabobi.