An daure budurwa mai kwacen babur
Wata budurwa ’yar shekara 18 mai suna A’ishatu Abdullahi da ke garin Gwagwalada a yankin Birnin Tarayya Abuja ta fara zaman shekara biyu a kurkuku bayan samunta da laifin yaudarar masu baburan acaba tana kwace masu babur. Hukuncin, wanda alkalin Kotun Majistire ta garin Gwagwalada, Mai Shari’a Ibrahm Yusuf ya yanke, ya biyo bayan korafin […]

Wata budurwa ’yar shekara 18 mai suna A’ishatu Abdullahi da ke garin Gwagwalada a yankin Birnin Tarayya Abuja ta fara zaman shekara biyu a kurkuku bayan samunta da laifin yaudarar masu baburan acaba tana kwace masu babur.
Hukuncin, wanda alkalin Kotun Majistire ta garin Gwagwalada, Mai Shari’a Ibrahm Yusuf ya yanke, ya biyo bayan korafin jami’in shigar da kara na ’yan sanda ne daga babban ofishinsu na garin su ka shigar kotun a kan yarinyar tare da wani abokin harkarta mai suna Muktar Garba a kan lamarin, bayan sun samu korafi daga wajen wasu ’yan acaba biyu.
Tun farko, jami’in dan sandan ya sanar da kotun cewa mutanen biyu sun tsayar da masu baburan hayan biyu da aka kiyasta kudinsu a kan Naira 260, sannan suka nemi su dauke su zuwa wani yanki da ke da karancin jama’a da ke cikin garin, inda wasu abokan huldarsu ke jiransu; ciki hadda wani mai suna Babangida da har zuwa lokacin yanke hukuncin ba a san inda yake ba.
“Bayan nan kun kwace baburan daga hannun masu shi. Wannan abin da kuka aikata laifi ne da ya saba wa doka ta 96 da 292 a tsarin dokoki na Finalkod, a saboda haka kun aikata laifi,” inji mai shari’a.
Da aka waiwaye su, mutanen biyu sun amince da aikata laifuffukan sannan suka bukaci kotun da ta yi masu sassauci. Mai shari’ar ya yanke masu hukuncin daurin shekara daya ba tare da zabin biyan tara ba, sannan ya yanke masu hukuncin wani daurin na shekara daya ko kuma zabin biyan diyyar Naira dubu 100 daga kowannensu, domin biyan masu baburan. An wuce da mutanen biyu zuwa gidan kurkukun garin Suleja.