An daure dalibin da ya saci kare wata 6 a gidan yari

Kotun ta bukaci ya biya tarar N20,000 da kuma diyyar N50,000 ko daurin watanni shida.

An daure dalibin da ya saci kare wata 6 a gidan yari

Karnuka

Wata kotu da ke zamanta a yankin  Kasuwan Nama da ke garin Jos, a jihar Filato ta yanke wa wani dalibi hukuncin daurin wata shida a gidan yari saboda satar karnuka biyu.

Bayan amsa laifin da matashin ya yi,  kwamitin alkalan da suka jagoranci shariar sun yanke masa hukuncin durain wata  uku ko biyan tarar N20,000.

Alkalan sun kuma bukaci ya biya diyyar N50,000 saboda satar karnukan, ko kuma ya sake shafe wasu watanni uku a daure.

Sun ce hukuncin da aka yanke wa dalibin mai shekara 15, zai zama izina ga masu yunkurin aikata irin laifi.

Tun da farko, lauyan da ya shigar da kara, Ibrahim Gokwat ya ce an kai kara ofishin ’yan sanda na Angwan Rogo a ranar 21 ga Janairu.

A cewar lauyan, darajar karnukan da dalibin ya sata ya kai N50,000 kuma hakan laifi a karkashin Sashe na 272 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Filato.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya