An daure dan jarida wata 4 a Ghana

A ranar Larabar makon jiya ne Kotun kolin kasar Ghana ta yanke wa wani dan jarida ma’aikacin gidan rediyon Muntie FM mai suna Salifu Masse da wadansu mutum biyu daurin wata hudu a gidan yari, dalilin wani shiri da su suka gabatar.A lokacin shirin, wanda  dan jaridar ya gayyato Alistair Tairo Nelson da Godwin Ako […]

An daure dan jarida wata 4 a Ghana
An daure dan jarida wata 4 a Ghana

A ranar Larabar makon jiya ne Kotun kolin kasar Ghana ta yanke wa wani dan jarida ma’aikacin gidan rediyon Muntie FM mai suna Salifu Masse da wadansu mutum biyu daurin wata hudu a gidan yari, dalilin wani shiri da su suka gabatar.
A lokacin shirin, wanda  dan jaridar ya gayyato Alistair Tairo Nelson da Godwin Ako Gunn. Bakin nasa  sun rika maganar batanci ga Babban Alkaliyar kasar Mai Shari’a Misis Georgina Theodora Wood da Mai Shari’a Sule Gbadegbe. Kuma bisa wannan ne aka tuhume su a gaban kotun.
A makon farko da aka gabatar da su a gaban kotun, kuma kotun ta cika makil da magoya bayansu,inda suka yi dafiti suna masu kiran a sallame su, saboda kamar yanda suka ce wsu sun yi maganganu da suka fi wannan, amma babu abin da akayi musu,suna masu yin misali da wani mamban majalisar dokoki na bangaren babban jam’iyyar adawa wato NPP, Honabul Kennedy Agyepong, wanda ya rinka kiran kabilar Akan su dan makamai su rinka kashe kabilar Ga da Ewe wadanda su ne suka fi ba jam’iyyar NDC mai mulki goyan baya, suka ce “bayan fadan wannan muguwar magana me aka yi masa.”
Masu nuna rashin goyan bayansu a kan matakin da kotun ta dauka sun nuna cewa shi dan majalisar ya fito fili yana zargin kwamishinan Hukuman Zabe Madam Charlotte Osei cewa “sai da ta bayar da kanta, sa’a nan aka ba ta wannan makamin da take rike da shi.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne alkalan kasar ke bikin tunawa da alkalai uku da ake yi wa kisan gila shekara 30 da suka wuce. Kuma a irin wannan rana ce Salifu ya gayyato Alistair da Godwin domin tattaunawa a kan karar hukumar zabe da alkalam kotun game da korafin da ’yan adawa ke yi cewa rajistan masu zaben kasar na cike da sunayen baki wadanda yawancinsu sun yi rijistan ne da katin ishuran kiwon lafiya, don haka sai lalle kotun ta bukaci hukumar zaben ta cire su daga kundin.
A kan haka ne suka yi shirin suna masu yi wa alkalan barazana cewa za a kashe su in har suka bi on rai game da wannan maganar ko da yake shi me gabatar da shirin bai fadi wani mugun abu ba. Sai dai laifinsa kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana, shi ne ya ba su kwarin gwiwa.
Kodayake  da aka gabatar da su a gaban kotun, sun nuna nadamarsu tare da bukatar kotun ta yafe musu. Bukatar da kotun ta yi biris da ita.