An daure dan luwadi shekara 12 a Jigawa

Babar Kotun Shari’a ta 4 da ke Dutse a Jihar Jigawa ta daure wani magidanci mai kimanin shekara 45 mai suna Nura Ahmed da ke kauyen Jigawar Tsada a karamar Hukumar Dutse shekara 12 saboda samunsa da laifin aikata luwadi da yaro dan shekara goma.Alkalin Kotun Mai shari’a Auwalu Ahmed Taura ne ya yanke wa […]

An daure dan luwadi shekara 12 a Jigawa
An daure dan luwadi shekara 12 a Jigawa

Babar Kotun Shari’a ta 4 da ke Dutse a Jihar Jigawa ta daure wani magidanci mai kimanin shekara 45 mai suna Nura Ahmed da ke kauyen Jigawar Tsada a karamar Hukumar Dutse shekara 12 saboda samunsa da laifin aikata luwadi da yaro dan shekara goma.
Alkalin Kotun Mai shari’a Auwalu Ahmed Taura ne ya yanke wa Nura Ahmed hukuncin a shekaranjiya Laraba, bayan da wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da gabatar da kwararan shaidu da bai musanta su a gaban kotun ba.
Mai shari’a Auwalu Ahmed ya ce kotun ta daure Nura Ahmed bisa dogaro da bayanan da ta samu daga ’yan sanda wadanda bai musanta ba a gaban kotun, saboda haka ne kotun ta yi masa hukuncin domin ya zama darasi ga masu irin wannan hali.
Mai shari’a Taura ya ce laifin da ake zargin Nura da aikatawa ya saba wa sahi na 284 na manyan laifuffuka. Ya ce kotun ta lura akwai yawaitar samun laifuffuka makamantan haka a jihar da suka hada da luwadi da yi wa yara kanana fyade.
Ya ce kotun ta ba wanda a ka yanke wa hukuncin damar daukaka kara zuwa nan da wata uku idan bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke masa ba.
Awata sabuwa kuma Kwamashinan Shari’a na Jihar Jigawa Barista Yakubu Abdullahi Ruba ya ce gwamnatin jihar ta yi wa wasu tsararru 14 afuwa. Goma daga cikin daurarrun an sake su ne daga gidan mazan da ake tsare da su sakamakon bincike da gwamnatin ta yi inda ta gano laifinsu bai wuce na zargin maita ko fada da juna ba.
Sauran hudun sassauta musu aka yi daga hukuncin kisa zuwa na daurin rai da rai saboda laifinsu ya hada da fashi da makami wadanda bayanai suka nuna cewa sun gyara halayensu sun zama mutane nagari.
Gwamna Lamido ya yi musu afuwa don murnar kewayowar ranar dimokuradiyya da aka yi a jiya Alhamis, inda ya ce gwamnatin ta yi amfani da sahi na 2021 da ya ba Gwamna damar saki ko yin afuwa ga daurarru.