An daure dan majalisa kan watsa labaran karya a Kwaddibuwa
Wata kotu a Kwaddibuwa (Ibory Coast) ta yanke hukuncin daurin shekara daya a kan dan majalisar kasar Alain Lobognon bisa samunsa da laifin watsa labaran karya da yunkurin tayar da zaune-tsaye. Kotun ta kuma ci tarar dan majalisar sefa (FCFA) dubu 300. An zarge shi da wallafa wasu sakonni ne a Tiwita wadanda ka iya […]
Wata kotu a Kwaddibuwa (Ibory Coast) ta yanke hukuncin daurin shekara daya a kan dan majalisar kasar Alain Lobognon bisa samunsa da laifin watsa labaran karya da yunkurin tayar da zaune-tsaye.
Kotun ta kuma ci tarar dan majalisar sefa (FCFA) dubu 300.
An zarge shi da wallafa wasu sakonni ne a Tiwita wadanda ka iya haddasa zanga-zanga.
Sai dai lauyan Alain Lobognon ya ce za su daukaka kara.
Lauyan, Affoussi Lamine Bamba, ya yi zargin cewa an yanke hukuncin ne domin cimma wani buri na siyasa yana mai cewa ‘“An dauki matakin ne kawai saboda Alain Lobognon yana da alaka ta musamman da Shugaban Majalisar Dokoki Mista Soro Guillaume.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.
Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami a tsakanin Shugaba Alassane Ouattara da Mista Soro Guillaume. Ranar Litinin Shugaba Ouattara ya ce a watan Fabrairu Mista Guillaume zai sauka daga mukaminsa.