An daure dan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda Fyade

Wani yaro dan shekara 17 zai yi zaman gidan yarin shekaru 14 saboda cin lalata wata dalibar kwalejin ilimi.  Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a Akure ce ta yanke wa yaron hukunci ne bayan an tabbatar da laifin. An fara gurfanar da wanda aka kama da laifin ne a watan Disambar 2021, […]

An daure dan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda Fyade

Wani mutum a kurkuku

Wani yaro dan shekara 17 zai yi zaman gidan yarin shekaru 14 saboda cin lalata wata dalibar kwalejin ilimi. 

Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a Akure ce ta yanke wa yaron hukunci ne bayan an tabbatar da laifin.

An fara gurfanar da wanda aka kama da laifin ne a watan Disambar 2021, bisa tuhume-tuhume biyu na cin zarafi da fyade, wanda a wancan lokacin yaron ya ki amsa laifinsa.

Lauyan mai shigar da kara, Dayo Kayode, ya sanar da kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 11 ga Maris 2021, da misalin karfe 5 na yamma.

A cewar masu gabatar da kara, laifukan sun ci karo da sashe na 60, da na 358 na kundin laifuffuka na Jihar Ondo, na shekarar 2016.

Da yake sanar hukuncin, Mai Shari’a Yemi Fasanmi, ya yanke wa yaron hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa kan laifin cin zarafi.

Sannan ya aka yanke masa shekaru 12 a gidan yari bisa laifin aikata fyade.

“Jimillar daurin shekaru 14 a gidan yari zai fara ne daga ranar farkon da aka kama wanda aka yanke wa hukuncin,” in ji alkakin.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta