An daure dan Zambabwe shekara 120 kan yada kanjamau a Amurka

Wata kotu a kasar Amurka ta daure wani dan kasar Zimbabwe mai suna Derick Nhekairo mai kimanin shekara 36 na tsawon shekara 120 a gidan kurkuku bayan da ta same shi da laifin yada cutar kanjamau ga wasu mata hudu a kasar.Derick Nhekairo wanda aka kama shi a watan Yulin bara bisa zargin aikata mugun […]

An daure dan Zambabwe shekara 120 kan yada kanjamau a Amurka

Derick NhekairoWata kotu a kasar Amurka ta daure wani dan kasar Zimbabwe mai suna Derick Nhekairo mai kimanin shekara 36 na tsawon shekara 120 a gidan kurkuku bayan da ta same shi da laifin yada cutar kanjamau ga wasu mata hudu a kasar.
Derick Nhekairo wanda aka kama shi a watan Yulin bara bisa zargin aikata mugun laifi daga farko ya musanta zargin da ake yi masa kafin ya canja ra’ayi daga baya.
Nhekairo wanda aka yanke wa hukuncin a ranar Alhamis din makon jiya, zai shafe shekara 60 daban-daban ne bisa samunsa da jawo mummunan rauni ga jikin dan Adam, yayin da zai shafe wasu shekara 60 guda biyu da shekara 20 hade da shekara 120 din.
Kuma kotun ta umarce shi ya biya tarar Dala dubu 32 (kimanin Naira miliyan biyar da dubu 120) kan tuhume-tuhumen hudu.
Mai gabatar da kara Lara Nodolf ta ce ta gabatar da kwararan hujjoji cewa Nhekairo ya cutar da matan hudu ta hanyar Tarawa da su alhali ya san yana dauke da kwayar cutar HIb mai haddasa kanjamau. Ta ce, ya furta cewa ya yi jima’i da mata 18 bayan ya harbu da cutar a shekarar 2002.
Nodolf ta ce yana da muhimmanci a hukunta Nhekairo saboda mutane da dama ba su san cewa babban laifi ba ne mutum ya yada kanjamau ga abokan jima’insa ba da saninsa ba.
Wadda Nhekairo ya fara yada wa kanjamau da ta kai rahotonsa ga sashin kiwon lafiya, ta shaida wa jaridar Telegram cewa, ta ji matukar dadi kan hukuncin. Ta ce, lokacin da ta harbu da cutar daga Nhekairo, cutar ta bunkasa zuwa cikakkiyar kanjamau, lamarin da ya kai ta gaza tafiya da kafafunta na kusan shekara daya.
Matar wadda yanzu take shan maganin kanjamau ta ce, cutar ta yi sauki, inda Cibiyar Yaki da Rigakafin Cututtuka masu Yaduwa ta Amurka ta ce duk da tana dauke da ita, barazanar harbar wasu da ita ta yi kasa sosai.  
Jihar Tedas dai tana daya daga cikin jihohin Amurka 35 da suka samu nasarar hukunta wadanda suka yada kanjamau da saninsu, kamat yadda bayanai suka nuna.