An daure Farfesa a kan laifin kwartanci

Babbar Kotun Majistare ta Kiyawa da ke Jihar Jigawa ta daure Farfesa Festus Dabid Kolo na sashin ilimi da ke Jami’a Ahmadu Bello da ke Zariya, wata biyu a gidan kurkuku ba tare da zabin biyan tara ba, bayan samunsa da laifin kwartanci.An tuhumi Farfesan ne da laifin aika wa matar aure sakonnin wayar hannu […]

An daure Farfesa a kan laifin kwartanci
An daure Farfesa a kan laifin kwartanci

Babbar Kotun Majistare ta Kiyawa da ke Jihar Jigawa ta daure Farfesa Festus Dabid Kolo na sashin ilimi da ke Jami’a Ahmadu Bello da ke Zariya, wata biyu a gidan kurkuku ba tare da zabin biyan tara ba, bayan samunsa da laifin kwartanci.
An tuhumi Farfesan ne da laifin aika wa matar aure sakonnin wayar hannu da suke da nasaba da batsa da soyayya, wanda hakan ya saba wa sashi na 389 na dokokin Final Kod.
Mai gabatar da kara a gaban kotun, Malam Mustapha Adamu ya shaida wa kotun cewa a ranar 21 ga watan Mayun da ya gabata, wani Muhammad Ghali mazaunin rukunin gidajen Takur da Dutse ya shaida wa Farfesa Festus Dabid Kolo na Jami’ar ABU da ke zariya cewa Bushura da yake nema matarsa aure ce kuma matarsa ce amma ya ci gaba da yi mata waya yana magana da ita tare da tura mata sakonnin soyayya.
Bayanan ’yan sanda na farko (FIR) sun nuna cewa an samu Farfesa Dabid Kolo dumu-dumu “a wani otel da ke danmusa a daki mai lamba 109 tare da matar Ghali bayan mijinta ya sanar da ’yan sanda halin da matarsa take fuskanta daga wurinka bayan ya yi ta yi maka gargadi a kan ka kiyayi matarsa amma ka kekasa kasa ka ki”.
Farfesan ya tabbatar wa kotun cewa bayanan da ’yan sanda suka rubuta a kansa gaskiya ne, kuma lauyoyinsa M.A. Gusau da R.A. Nwande sun ce Farfesan mai shekara 60 a duniya ya amince da aikata laifin, amma suna rokon kotun ta yi masa sassauci a kan laifin da ake tuhumarsa kasancewar yana da iyalai masu yawa wadanda a kansa suka dogara, idan aka daure shi tsawon wani lokaci mai tsawo suna iya shiga wani muwuyacin halin rayuwa.
Da yake zartar da hukunci Alkalin Kotun, Mai shari’a Muhammed Musa Kaugama ya daure Farfesan a gidan maza na tsawon wata biyu bisa da laifin da ake zarginsa kasancewar wannan shi ne laifinsa na farko da ake tuhumarsa a gaban kotu ba tare da zabin biyan tara ba.
Wani na kusa da hukumar jami’ar da wakilinmu ya tattauna da shi da shi ma bai so a ambaci sunnansa ba, ya ce lallai sun sami takarda a rubuce cewar ’yan sanda sun kama Farfesa Kolo, kuma har wata kotu ta daure shi ba tare da zabin biyan tara ba. Ya ce tuni hukumar jami’ar ta gabatar da takardar wajen jami’an tsaronta domin gudanar da bincike a kan lamarin, kuma sakamakon abin da suka bincika shi ne za a dauki matakin da ya kamata a kai, domi jami’ar tana da nata dokokin da take ladabtar da duk wanda ya aikata irin wannan laifin.