An daure Farfesan da ya nemi lalata da daliba shekara biyu

Malamin Jami’ar Obafemi Awolowon nan, Farfesa Richard Iyiola Akindele zai shafe shekara biyu a gidan kaso kan samunsa da kokarin yin lalata da dalibarsa, Monica Osagie wacce ya yi wa alkawarin gyara sakamakon jarrabawarta. Babbar Kotun Tarayya ce ta yanke masa wannan hukunci a zamanta na ranar Litinin a Osogbo, Jihar Osun. Kafin a yanke […]

An daure Farfesan da ya nemi lalata da daliba shekara biyu

Malamin Jami’ar Obafemi Awolowon nan, Farfesa Richard Iyiola Akindele zai shafe shekara biyu a gidan kaso kan samunsa da kokarin yin lalata da dalibarsa, Monica Osagie wacce ya yi wa alkawarin gyara sakamakon jarrabawarta. Babbar Kotun Tarayya ce ta yanke masa wannan hukunci a zamanta na ranar Litinin a Osogbo, Jihar Osun.

Kafin a yanke masa hukunci, Farfesa Akindele bai amince da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba, amma a zaman kotun na ranar Litinin ya amince da aikata laifin.

Da yake mika rokon kotun ta dakatar da batun yanke hukunci ga mai laifin, domin a yi zaman gyara al’amarin a wajen kotu, lauyan malamin, Francis Omotosho ya karanto wa kotun wasu misalai da suka sa yake yin rokon.

Misalan sun hada da cewa, Farfesa Akindele ya rasa aikinsa dalilin aukuwar lamarin, wanda ya zame masa darasi. Kuma Jami’ar OAU ta gane kuskurenta a kan takardar jarrabawar daliba Monica wanda yanzu haka jami’ar ta yanke shawarar biyanta diyya ga dalibar. Kuma hukumar jami’ar ta kammala shirin mayar da ofisoshin malamai zuwa ginin gilashi da ake iya hangen komai daga waje don hana aukuwar irin haka a nan gaba.

Bayan sauraron rokon ne Alkalin Kotun Mai shari’a Maureen Onyetenu ta yi tambaya ga Lauya Omotosho cewa “Kana zaton suna yin abin a cikin ofis ne? Suna zuwa otal ne.” Saboda haka ta ki amincewa da rokon saboda illar da irin wannan matsala ta yin lalata da dalibai da malaman makaranta ke yi take haifarwa.

Mai shari’a Maureen Onyetenu, ta nuna takaici kan yawaitar lalata da dalibai mata da malamai ke yi a manya da kananan makarantun kasar nan. Ta ce “Muna tura ’ya’yanmu zuwa makaranta su dawo suna gaya mana cewa malamansu suna neman lalata da su. Hatta makarantun firamare ba su tsira ba. Ba za mu ci gaba da haka ba. Wajibi ne a yi amfani da hukuncin da zai zama darasin don kawo karshen matsalar. Wannan al’amarin yana ci gaba da yawaita saboda ba a yi amfani da wani hukunci  a matsayin darasi ba. Lokaci ya yi da kotuna za su dauki matakin kare mutuncin kananan yara musamman dalibai mata.”

Lauyan Hukumar ICPC da ta shigar da karar, Mista Shogunle Adenekan ya roki kotun ta kwace wayar hannu mallakar Farfesa Richard Akindele ta koma mallakar Gwamnatin Tarayya kuma ta mayar wa daliba Monica Osagie da wayarta da ta yi amfani da ita a boye wajen daukar hoton bidiyon kalaman malamin a lokacin da suke cikin daki ba tare da saninsa ba.

Bayan sauraron bayanan lauyoyin biyu Alkali Maureen Onyetenu ta daure Farfesa Richard Akindele shekara biyu. Kuma ta bayar da umarnin mayar wa  Monica wayarta tare da kwace wayar malamin don ta zama mallakar Gwamnatin Tarayya.