An daure likita shekara 25 don laifin lalata yaro

A ranar Litinin din makon jiya ne wata kuto a birnin Accra ta saurari shari’ar Sulley Ali Gabass, wani likita wanda ake zarge da lalata wani yaro dan shekara 16, inda aka yanke masa daurin shekara 25 a gidan kaso bayan kotun ta same shi da laifi.Yaro da aka lalata dai dalibi ne a wata […]

An daure likita shekara 25 don laifin lalata yaro
An daure likita shekara 25 don laifin lalata yaro

A ranar Litinin din makon jiya ne wata kuto a birnin Accra ta saurari shari’ar Sulley Ali Gabass, wani likita wanda ake zarge da lalata wani yaro dan shekara 16, inda aka yanke masa daurin shekara 25 a gidan kaso bayan kotun ta same shi da laifi.
Yaro da aka lalata dai dalibi ne a wata unguwa da ake cewa kira Kasoa, yayin da shi Ali Gabass sananen likita ne a babban asbitin Jihar Effia Nkwanta.
Kamar yadda bayanai suka nuna, a watan Satumbar shekarar 2013 ne suka hadu a shafin sada zumunta na Facebook, inda suka kulla abota. Daga nan suka fara hurda ta wayar salula har na tsawon kimanin wata guda. Bayan wannan lokacin ne  Likitan ya shirya haduwarsa da yaron a Babban Kasuwan unguwar Kasoa, inda binciken ya nuna cewa “ya yi amfani da yaron ne a cikin motarsa.”
Har ila yau,  Mai Shiri’ar ta ce: “ A ranar  28 ga watan Disambar shekarar 2013 da karfe 7 na yamma sun sake saduwa a nan wuri guda, Ali Gabass ya sake yin amfani da yaron, a nan ne ya ba shi kyautar waya samfarin Samsun Galady da kudi 20 sidi. Bayan saduwar  ne kuma yaron ya fara ciwo, da ya shaida masa, sai  ya ba shi Parasitamol. Hakazalika, a watan Fabrairun bara ya sake  lalata da yaron.
Jami’an ’yan sanda dai sun kama likitan ne bisa zargin ya lalata yaron bayan tashar Joy FM ta bakin wani Manaseh Awuni Azure ta sanar da zargin.