An daure mai gadi wata 3 saboda satar naman miya a Abuja

Kotun ta bai wa mai gadin damar biyan tarar 20,000.

An daure mai gadi wata 3 saboda satar naman miya a Abuja

Daurin Kotu

Wata kotu da ke yankin Dei-Dei a Abuja, ta daure wani mai gadi mai suna Okoh Richard tsawon watanni uku a gidan yari sakamakon satar naman miya da lemo a wani otal da ya ke aiki.

Richard, wanda ya ke aikin gadi a otal din Edimony a Abuja, an gurfanar da shi a gaban Kuliya da laifin dan hali.

Sai dai alkalin kotun Sulyman Ola ya bai wa Richard damar biyan tara 20,000.

Kazalika alkalin ya gargadi wanda ake tuhuma da ya kasance mai da’a.

Daga bisani Richard ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kana ya roki kotun da ta yi masa sassauci wajen yanke hukunci.

Da farko lauyan masu gabatar da kara, Mista Olaonipekun Babajide, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Mista Echezona Mogboma ne ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda na Dawaki da ke Abuja  a ranar 10 ga watan Maris.

Babajide, ya ce wanda ake tuhuma da laifin yana aiki a otal din Edimony da ke yankin Katampe a matsayin mai gadi.

Ya ce mai gadin ya fasa tagar dakin girkin  otal din, inda ya saci nama da lemuka.

Ya ce wanda ake tuhumar ya kuma yi yunkurin kutsawa cikin ofishin manajan otal din Edimony, amma asirinsa ya tonu.