An daure mai satar jakar mata a asibiti
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge Waje a birnin Kano ta daure wata budurwa bisa samunta da laifin sace jakukunan mata a Asibitin Malam Aminu Kano. Dubun budurwar mai suna Binta Muhammad ya cika ne a yayin da ta sace jakar wata mata da ta je ganin likita a asibitin, inda aka kama ta tare […]
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge Waje a birnin Kano ta daure wata budurwa bisa samunta da laifin sace jakukunan mata a Asibitin Malam Aminu Kano.
Dubun budurwar mai suna Binta Muhammad ya cika ne a yayin da ta sace jakar wata mata da ta je ganin likita a asibitin, inda aka kama ta tare da damka ta ga ’yan sanda.
Hukumar asibitin ta ce ta dade tana samun rahotannin yadda ake sace jakunkunan mata masu jinya da wadanda ke shiga asibitin don ganin likita.
Wacce ake zargin ta amsa laifinta inda ta ce wata mata ce take aikenta sato jakunkunan matan a asibiti, sai dai matar ta musanta hakan, inda ta ce abin da ta sani kawai shi ne budurwar na kawo mata jaka tana saye ba tare da ta san na sata ba ne.
Alkalin kotun Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ne ya yanke wa budurwar hukuncin daurin shekara biyu ko biyan tarar Naira dubu 20 da kuma daurin wata biyu ba tare da zabin biyan tara ba.
A wani labarin kuma Kotun Shari’ar Musulunci ta Uku da ke kofar Kudu a birnin Kano ta bayar da umarni a tsare wanda ake zargi da bugawa da raba takardar daukar aiki ta jabu ga jama’a a Jihar Kano.
Ana zargin mutum mai suna Mu’allim Muhamamd ’Yankaba da raba takardar aiki ta jabu ga wasu ma’aikatan lafiya tare da tura su asibitocin gwamnati bayan ya karbi makudan kudi daga hannunsu.
Da aka karanta masa laifin da ake zarginsa, Mu’allim ya amsa laifinsa, laifin da dan sanda mai gabatar da kara Yusuf Garba ya shaida wa kotun cewa ya saba wa sashi na 342 da 253 na Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Sani Sarki Yola ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin zuwa ranar 29 ga wannan wata.