An daure makahon da ya saci ’yar jagora

Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano ta daure wani makaho shekara daya a kurkuku bisa samunsa da laifin sacewa tare da boye wata yarinya don ta zame masa ’yar jagora.dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa mahaifin yarinyar mai suna Ibrahim D. Inusa […]

An daure makahon da ya saci ’yar jagora
An daure makahon da ya saci ’yar jagora

Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano ta daure wani makaho shekara daya a kurkuku bisa samunsa da laifin sacewa tare da boye wata yarinya don ta zame masa ’yar jagora.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Yusuf Bello ya shaida wa kotun cewa mahaifin yarinyar mai suna Ibrahim D. Inusa mazaunin Unguwar Hausawa ne ya shigar da kara cewa makahon mai suna Isah dahiru wanda suke zaune unguwa daya da shi ya sace ’yarsa mai suna Maryam Ibrahim mai kimanin shekara 11 inda ya tafi da ita Ibadan a matsayin ’yar jagorarsa.
dan sandan ya kara da cewa “Sakamakon baza cigiyar yarinyar da aka yi ya sa wasu sojoji suka kama makahon bayan yarinyar ta fada hannunsu a lokacin da ta nemi uban dakin nata ta rasa. Daga nan ne wani ya dauke ta ya kai ta barikin sojjoji inda su kuma suka yi bincike har suka gano iyayenta inda mahaifinta ya je ya taho da ita Kano,”
Sufeto Bello ya bayyana wa kotun cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka kama wanda ake zargin da irin wannan laifi ba, domin ko a bara wata kotun ta yanke masa hukunci a kan irin haka.    
Ya ce laifin da ake zargin makahon da shi ya saba wa sashi na 175 na kundin shari’ar Final kod.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya nemi kotu ta yi masa sassauci cikin hukuncin da za ta yanke masa.
Alkalin kotun Mai shari’a Kabir Muhamamd Imam ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan maza tsawon shekara guda ba tare da zabin biyan tara ba.