An daure Maman Boko Haram shekara 10 a kurkuku

An daure Aisah Alkali Wakil kan laifin damfara ta Naira miliyan 40

An daure Maman Boko Haram shekara 10 a kurkuku

Maman Boko Haram

Babbar Kotun Jihar Borno ta yanke wa Aisha Alkali Wakil, wadda aka fi sani da Maman Boko Haram hukuncin daurin shekaru 10 a kan zambar Naira miliyan 40.

Mai shari’a Umaru Fadawu ya daure Maman Boko Haram da wasu  mutane biyu, Tahiru Saidu Daura da kuma Yarima Lawal Soyade ne bayan an same su da laifukan da suka shafi hada baki da kuma damfara ta N40,000,000.00.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ce ta fara gurfanar da su a shekarar 2020 a gaban kotun da ke zamanta a Maiduguri, bayan cikakken bincike.

Wani mai suna Bashir Muhammad ne ya kai wa EFCC korafi cewa sun damfare shi Naira miliyan 40 ba ya ba su kwangilar samar da injinan daukar hoton X-ray guda biyar tare da na’uarar ba da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga wata kungiya mai zaman kanta, Complete Care and Aid Foundation.

A karshe, ba su ba da injinan ba kuma ba su dawo da kuɗin kwangilar ba, amma kuma sun musanta zargin lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.

Lauyan mai gabatar da kara, AI Arogha ya gabatar da shaidu hudu tare da gabatar da hujjoji 17 a gaban kotun.

Sakamakon haka, Mai Shari’a Fadawu ya yanke musu hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari tare da ba su umarnin biyan kundin.http://google.com