An daure manomi shekara 15 kan laifin boye bayanan ayyukan Boko Haram
Alkali Binta Fatimah Nyako ta ba da umarnin cewa hukuncin daurin shekaru 15 ya fara tun daga shekarar 2013 lokacin da aka kama wanda ake zargin aka kuma tsare shi.
An yanke wa wani manomi mai shekaru 55, Ali Mustapha, hukuncin daurin shekaru 15 ba tare da zabin tara ba saboda boye bayanai kan munanan ayyukan kungiyar Boko Haram a kauyensu na Katara da ke Jihar Borno.
An gurfanar da manomin ne tun shekarar 2013 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hannun Babban Lauyan Tarayya, Prince Lateef Fagbemi (SAN), inda ya amsa laifinsa.
Saboda haka, Alkali Binta Fatimah Nyako ta yanke masa hukuncin shekaru 15 ba tare da zabin tara ba.
Alkali Binta Fatimah Nyako ta ba da umarnin cewa hukuncin daurin shekaru 15 ya fara tun daga shekarar 2013 lokacin da aka kama wanda ake zargin aka kuma tsare shi.