An daure masu fyade shekara takwas

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu magidanta uku hukuncin daurin shekara takwas-takwas a kurkuku bisa samunsu da laifin yi wa wasu kananan ’yan mata fyade.Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Muhammad Salisu Gambo da Madu Muhammad da Umar Muhammad wadanda dukkansu aka samu da yi wa wasu yara mata […]

An daure masu fyade shekara takwas
An daure masu fyade shekara takwas

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu magidanta uku hukuncin daurin shekara takwas-takwas a kurkuku bisa samunsu da laifin yi wa wasu kananan ’yan mata fyade.
Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Muhammad Salisu Gambo da Madu Muhammad da Umar Muhammad wadanda dukkansu aka samu da yi wa wasu yara mata daban-daban fyade.
Da take yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a Dije Aboki ta ce za a hada wa masu laifin da aiki mai tsanani a tsawon zamansu a kurkuku.