An daure matar da ta sa yara shan amansu
An daure wata uwa mai rainon yara da ta azabtar da kananan yara ta hanyar tilasta musu shan amai. Matar mai suna Rachel Lessels ta yi kuka a kotu bayan da aka yanke mata hukuncin daurin wata 14 a gidan yari, bayan da wasu alkalai suka same ta da laifi. Yadda barawon kananan yara ya […]
An daure wata uwa mai rainon yara da ta azabtar da kananan yara ta hanyar tilasta musu shan amai.
Matar mai suna Rachel Lessels ta yi kuka a kotu bayan da aka yanke mata hukuncin daurin wata 14 a gidan yari, bayan da wasu alkalai suka same ta da laifi.
- Yadda barawon kananan yara ya fada komar ’yan sanda
- Abin da fim din Sanda zango na biyu ya kunsa —Abale
Kotun ta yanke hukuncin cewa, matar ta yi ta zaluntar yaran da suke hannunta sama da shekara uku.
A lokacin shari’ar, alkalan sun gano cewa, wadanda Lessels ta azabtar suna fama da ciwo na tsawon lokaci sakamakon zaluncin da ta yi musu.
Laifuffukan sun shafi mutum biyu da aka azabtar wadanda yara ne a lokacin da aka ci zarafinsu, kamar yadda Daily Record ta ruwaito.
Alkali Paul Brown ya ce: “Wadannan munanan laifuffuka ne a kan yaran da ba su da kariya da suke hannun wadda take rainonsu.
“Ya kamata wadda ta aikata hakan ta kasance mai amana. Don haka, babu wata makoma ga mai laifin sai gidan yari.”
Wadanda abin ya shafa sun shaida wa alkalan kotun Dundee Sheriff cewa, an nuna wa yaran rashin tausayi yayin da suke hannunta.
A yayin shari’ar ta kwanak uku, wani matashi mai shekara 18, ya ce Rachel ta tilasta masa ya sha amansa bayan ya yi aman abincinsa.
“Ina kuka sai Rachel ta ce za a fitar da ni daga aikin tsarin zamantakewa idan ban sha ba,” inji shi.
Wata wadda abin ya rutsa da ita ta shaida wa kotu wannan lamari sai jikinta ya yi sanyi ta rike kanta don ta kasa numfashi.
A yayin shari’ar, wani wanda abin ya shafa ya ce, Rachel ta ja al’aurarsa, ta tilasta masa dora kansa a kan wani benci, sannan ta sa shi fita tsirara zuwa cikin motarta.