An daure matar da ta saci Naira miliyan takwas shekara 266
An daure wata ma’aikaciyar fitaccen gidan abinci nan na Sweet Sensation, mai suna Oluremi Olayinka shekara 266, sakamakon samunta da laifin sace Naira miliyan takwas mallakar gidan abincin. A shekaranjiya Laraba ne Alkalin Babbar Kotun Jihar Ogun Mai shari’a A. A. Akinyemi ya daure Oluremi Olayinka, inda ya ce abin da ta aikata ya saba […]
An daure wata ma’aikaciyar fitaccen gidan abinci nan na Sweet Sensation, mai suna Oluremi Olayinka shekara 266, sakamakon samunta da laifin sace Naira miliyan takwas mallakar gidan abincin.
A shekaranjiya Laraba ne Alkalin Babbar Kotun Jihar Ogun Mai shari’a A. A. Akinyemi ya daure Oluremi Olayinka, inda ya ce abin da ta aikata ya saba wa sassa na 390 (6) (7) da (8), 467 da kuma 468 na kundin manyan laifuffuka na Jihar Ogun.
Kotun ta samu Olayinka da aikata laifuffuka 34 da aka tuhume ta, inda ta yanke mata dauren shekara bakwai-bakwai kan tuhume-tuhume 30 da kuma shekara goma sha hurhudu kan sauran tuhume-tuhume hudu, jimilla shekara 266, sai dai za ta yi zaman Kason ne a jere, wato a karshe za ta shekara 14 ke nan a gidan maza.
Bayan haka Mai shari’a Akinyemi ya umarce ta da ta mayar da kudin da ta sata ga mai su.
A ranar 13 ga Mayun bara ne aka gabatar da Olayinka a gaban Mai shari’a Akinyemi, bayan da aka kai kukan ta sace Naira miliyan takwas da ta karba a madadin gidan abincin.
Lokacin da aka tunkare ta dazargin ta amince da aikata laifin amma sai ta sauya ra’ayi lokacin da aka gurfanar da ita a gaban kotu.
A yayin shari’ar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ta gabatar da shaidu hudu da takardu shaida 16 don tabbatar da zargin da ake yi mata, kuma da su ne alkalin ya dogara wajen yanke mata wannan hukunci.