An daure matar da ta yi wa ayar Al Kur’ani izgili a Morocco

An yanke mata hukunci kan izgilin da ta yi ta hanyar kwaikwayon ayar Al Kur’ani.

An daure matar da ta yi wa ayar Al Kur’ani izgili a Morocco

Rabat, babban birnin Morocco

Rahotanni sun ce wata kotu a Kasar Morocco ta yanke wa wata mata ’yar kasar amma asalin Italiya hukuncin daurin shekaru uku da rabi a gidan yari.

Wannan hukunci na zuwa ne bayan samun matar da cin mutuncin addinin Islama cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook da ke izgili ta hanyar kwaikwayon ayar Al Kur’ani.

Mahaifin matar mai shekara 23, ya ce an kama ta a filin jirgin sama na Rabat, babban birnin kasar, lokacin da take sauka daga Faransa inda take karatu.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, wata kungiyar addini a Marrakesh ce ta kai karar ta ga hukumomi wanda har ya kai ga yanke mata hukuncin.

Zaɓen Edo: INEC ta dakatar da tattara sakamako

Zaɓen Edo: Magoya bayan PDP sun fara zanga-zanga 

Kwalara ta yi ajalin mutum 12 a Adamawa

Tsadar Rayuwa: Matar Tinubu ta raba wa ɗalibai littafan rubutu a Nasawara