An daure matasa bisa laifin sayar da wiwi a Jigawa
Kotun Lardi ta shari’ar Musulunci da ke Dutse a karkashin Mai shari’a Ibrahim Yahaya Yayari ta daure wani matashi shekara biyu a gidan maza ko tarar Naira dubu shida saboda samunsa da laifin sayar da tabar wiwi da shan tabar. Haka shi ma matashi mai suna Ukashatu Ya’u Dogo da ke karamar Hukumar Garki, Jihar […]
Kotun Lardi ta shari’ar Musulunci da ke Dutse a karkashin Mai shari’a Ibrahim Yahaya Yayari ta daure wani matashi shekara biyu a gidan maza ko tarar Naira dubu shida saboda samunsa da laifin sayar da tabar wiwi da shan tabar. Haka shi ma matashi mai suna Ukashatu Ya’u Dogo da ke karamar Hukumar Garki, Jihar Jigawa.
Kamar yadda aka gabatar da batun a kotu, ’yan sanda ne suka kama matashi na biyu da tabar wiwi har dauri 50 kuma aka gabatar da ita gaban alkali a matsayin shaida.
A wata sabuwa kuma, wani matashi mai suna Adamu Aliyu Kudai, ya yi wa matarsa Asma’u Adamu Gombe dukan kawo wuka da wayar kyabul har ta kai ta ga kwantawa a asibiti. Lamarin da ya sa ’yan sanda suka kama mijin suka gabatar da shi a gaban kotun ta shari’ar Musulunci. Wanda ake tuhumar dai ya amsa laifinsa, inda ya ce bulala biyar kawai ya yi mata da mari biyu. Ya kuma tabbatar wa kotu cewa ba ta da lafiya tsawon wata shida amma bai taba zuwa ya duba ta ba. Sai dai kuma ya nemi kotun ta yi masa sassauci a kan laifin da ya aikata.
A yayin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Ibrahim ya ce laifin da Adamu ya aikata ya saba wa shari’ar Musulunci saboda haka kotun ta daure shi wata shida a gidan maza ko kuma ya biya tarar Naira dubu 15. Kuma kotun ta umarce shi da ya biya matar tasa kudin magani da ta kashe, Naira dubu 50.