An daure matasa hudu bisa lalata da matar aure
Babbar kotun shari’ar Musulinci ta Jihar Jigawa ta daure wasu matasa hudu da aka tuhuma da laifin lallashin matar aure suka aikata fasadi da ita a wata maboya, a yayin da kuma ’yan sanda suke kan neman mutun daya da ya tsere. Matasan hudu sun shiga hannun dogarawan karamar Hukumar Kiyawa a makon jiya, inda […]
Babbar kotun shari’ar Musulinci ta Jihar Jigawa ta daure wasu matasa hudu da aka tuhuma da laifin lallashin matar aure suka aikata fasadi da ita a wata maboya, a yayin da kuma ’yan sanda suke kan neman mutun daya da ya tsere.
Matasan hudu sun shiga hannun dogarawan karamar Hukumar Kiyawa a makon jiya, inda su kuma suka mika su ga ’yan sandan yankin, wadanda suka gabatar da su a gaban alkali.
Mai shari’a Ibrahim Yayari ya ce kotunsa ta daure matasan hudu na tsawon shekara daya a gidan maza ko kuma zabin tarar Naira dubu 20 kowannensu. Zun zabi biyan tarar, inda nan take suka biya, suka fanshi kawunansu.
Matasan da abin ya shafa sun hada da Yahaya Hassan da Umaru da Mahadi Zubairu da Tukur Musa. A yayin shari’ar dai, sun yi ikirari da bakinsu cewa sun aikata laifin da aka tuhume su da shi. Haka kuma, ’yan sanda suna neman matashin daya da ya gudu, mai suna Suleiman saboda shi ma ya aikata wancan laifin tare da wadancan matasa hudu.
Matar mai suna Hauwa Sani, ta tabbatar wa kotu cewa, duk mutanen da suka bayyana a gaban alkali da shi wancan da ake zargin ya gudu, dukansu sun aikata abin da ake tuhumarsu da shi ta hanyar yaudararta, alhalin tana matar aure. Saboda haka kotu ta ce za ta ci gaba da Tukur Musa, daya daga cikin matasan 4 da suka fanshi kansu a kotun saboda ana zargin shi ne ya boye Suleiman, ya ki fadar inda yake saboda haka za a ci gaba da tuhumarsa a mako mai zuwa a gaban kotu.
A wata sabuwa kuma, alkalin ya daure wani matashi mai kimanin shekaru 35, Musa Nasa’adu da ke kauyan Jiwan Tudu saboda laifin lallashin Habi Isma’il, yana kokarin yin lalata da ita, alhalin ya san matar aure ce.
Bayan dogayen tambayoyi da alkaline ya yi wa wanda ake tuhumar ya kasa kare kansa, sai ya sa ’yan sanda suka ingiza keyarsa zuwa kurkuku, kafin kotu ta samu damar kammala bincike a kan shari’ar.