An daure matasa kan satar wayar fitilun titi
Kotun Majistare Mai lamba 57 da ke Nomansland a birnin Kano ta bayar da umarnin daure wadansu matasa uku bisa zarginsu da barnatawa da sace wayoyin lantarki a kofar shiga Jami’ar Northwest da ke titin Kofar Kansakali a Kano. Takardar kara ta bayyana cewa jami’an sintiri da ke yankin ne suka kama matasan a lokacin […]
Kotun Majistare Mai lamba 57 da ke Nomansland a birnin Kano ta bayar da umarnin daure wadansu matasa uku bisa zarginsu da barnatawa da sace wayoyin lantarki a kofar shiga Jami’ar Northwest da ke titin Kofar Kansakali a Kano.
Takardar kara ta bayyana cewa jami’an sintiri da ke yankin ne suka kama matasan a lokacin da suke kokarin tumbuke wayoyin lantarki da ke haskaka fitilun kan titin a kusa da Jami’ar North-West inda kuma suka damka su ga ’yan sandan farin kaya da ke Jihar Kano.
Mai gabtar da karar ya shaida wa kotun cewa matasan da ake zargi da aikata wancan laifi sun hada da Abdulmutallib Lawan da Rabi’u A. da Salisu da Aliyu Lawan. Kuma lokacin da ake gudanar da bincike sun yi ikrarin cewa ba sau sun sha sace wayoyin lantarkin fitilun titi musamman wadanda ke kusa da Jami’ar North-West inda kuma suke kai wa wadansu mutane a Kasuwar Kurmi suna saye.
Lokacin da aka karanta wa wadanda ake zargin takardar karar, dukansu sun amsa laifuffukan da ake tuhumarsu da shi na hadin baki da sata, laifuffukan da suka saba da sashe na 97 da 287na kundin shari’a na Final Kod.
Alkalin kotun Mai Shari’a Haulatu Magaji Kankarofi ta daure wadanda ake zargin a kurkuku na tsawon wata shida ko biyan tarar Naira dubu 30.