An daure matashin da ya zagi mahaifinsa

A ranar Litinin da ta gabata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari a birnin Kano ta daure wani matashi mai kimanin shekara 23 mazaunin Unguwar Tudun Murtala wata  15 a kurkuku saboda samunsa da laifin zagin mahaifinsa da kuma yanka dabbobinsa ba tare da yardarsa ba. A ranar 9 ga Mayun bana ne Malam […]

An daure matashin da ya zagi mahaifinsa
An daure matashin da ya zagi mahaifinsa

A ranar Litinin da ta gabata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari a birnin Kano ta daure wani matashi mai kimanin shekara 23 mazaunin Unguwar Tudun Murtala wata  15 a kurkuku saboda samunsa da laifin zagin mahaifinsa da kuma yanka dabbobinsa ba tare da yardarsa ba. A ranar 9 ga Mayun bana ne Malam Abubakar Abdullahi ya kai karar dansa mai suna dahe Abubakar inda yake zarginsa da zaginsa da amfani da wuka wajen yanka tinkiyoyi biyu daga cikin tumakansa da kudinsu ya kai Naira dubu 30 saboda ya yi wa dan fada game da mummunar dabi’arsa.
Lokacin da aka karanta wa wanda ake zargi laifinsa ya masa duk abin da takardar kara ta kunsa da ya hada da zagi da mallakar makami da kuma tu’ammali da miyagun kwayoyi, inda ya nemi kotun ta yi masa sauki wajen yanke masa hukunci.
A lokacin da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ya daure mai laifin wata 15 a gidan maza ko kuma zabin biyan tarar Naira dubu 15.