An daure saurayin da ke kwana a dakin budurwarsa

An gurfanar da wani matashi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Zaki a Kano bisa zarginsa da kutsa kai gidan iyayen wata budurwarsa da tsakar dare ya kwana a dakinta.dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Yusuf Saleh ya shaida wa kotun cewa saurayin mai suna Usman Aminu yakan bi dare ya shiga […]

An daure saurayin da ke kwana a dakin budurwarsa
An daure saurayin da ke kwana a dakin budurwarsa

An gurfanar da wani matashi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Zaki a Kano bisa zarginsa da kutsa kai gidan iyayen wata budurwarsa da tsakar dare ya kwana a dakinta.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Yusuf Saleh ya shaida wa kotun cewa saurayin mai suna Usman Aminu yakan bi dare ya shiga gidan su budurwar ya shiga dakinta sannan kuma su kulle dakin iyayensu ta waje.
Hajiya Hafsatu Hamisu ita ce matar gidan, ta bayyana wa kotu cewa asirin saurayin ya tonu ne a daidai lokacin da ta fito da tsakar dare don ta kashe injin janaretan gidan, a nan ne ta leka dakin ’yarta inda take ta ga wani kato kwance a kan gadon ’yartata.
Da kotun ta waiwayi saurayin ya amsa laifinsa inda ya bayyana wa kotun cewa shi saurayin yarinyar gidan ne kuma ita yarinyar ce ke gayyato shi idan dare ya yi sai ta yi masa waya. Shi kuma idan ya zo sai ya kukkule sauran dakunan gidan ta waje don kada mutanen gidan su fito.
Sufeto Yusuf Saleh ya roki kotun da ta hukunta wanda ake zargin tunda dai ya amsa laifinsa.
Yayin da take yanke hukunci Alkalin Kotun Mai shari’a Binta Muhamamd Ahmad ta daure matashin wata hudu ba tare da zabin tara ba. Sai kuma daurin wata biyu ko kuma biyan tarar Naira dubu goma kan laifi na biyu.