An daure shi a gidan yari saboda zagin tutar China
Matashin zai yi zaman jarun saboda wulakanta tutar kasar China
Kotu ta yanke wani dan gwagwarmaya hukuncin daurin wata hudu a kurkuku saboda samun sa da laifin wulakanta tutar kasar China.
Kotun ta kama Tony Chung da lafin cin mutuncin tutar kasar China a lokacin wata zanga-zanga ofishin gwamantin kasar, inda ya yayyaga tutar kasar ya kuma jefar.
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- An cafke wadanda suka shirya casun jima’i a Kaduna
- Kisan da mata ke wa mazansu a kasar Hausa
Laifin nasa na da hukuncin daurin da zai iay kai wa shekara hudu a gidan yari.
A zaman Kotun Majistaren na ranar Talata, ta kuma kama Chung da laifin shiga haramtacciyar zanga-zangar da a lokacin ne yaga tutar kasar.
A yanke wa Tony Chung hukuncin ne daga cikin wasu mutanen da ke fuskantar zargin neman raba kan kasar China da kuma yada kalaman batanci.
Wanda aka yanke wa hukuncin dalibi ne mai shekara 19 da ke fafutukar samun ’yancin Hong Kong daga China.
A watan Oktoba ne jami’an tsaro suka kama shi a lokacin da yake kokarin neman mafaka daga Ofishin Jakadancin Amurka da ke Hong Kong.