An daure shi a kan satar waya da kudin matar da ta yi hatsari

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Unguwar Kurna, Jihar Kano ta daure wani matashi shekara guda a gidan kurkuku sakamakon samunsa da laifin satar wayar hannu da kuma wasu kudade, mallakar wata mata da ta yi hatsari. Tun da farko wata mata ce mai suna Mariya Musa ta yi karar matashin mai suna Auwalu Saminu bisa […]

An daure shi a kan satar waya da kudin matar da ta yi hatsari

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Unguwar Kurna, Jihar Kano ta daure wani matashi shekara guda a gidan kurkuku sakamakon samunsa da laifin satar wayar hannu da kuma wasu kudade, mallakar wata mata da ta yi hatsari.

Tun da farko wata mata ce mai suna Mariya Musa ta yi karar matashin mai suna Auwalu Saminu bisa zarginsa da yi mata satar waya da kuma wasu kudade a lokacin da suka yi hatsarin mota a Unguwar kofar Dawanau. “Bayan da hatsarin ya abku sai wanann matashi ya rugo a guje da nufin zai kawo mana agaji amma sai ya buge da satar waya tare da kudina da suka kai Naira dubu 20,” inji ta.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce tsautsayi ne ya kai shi ga aikata haka.

Alkalin Kotun Mai shari’a Halhalatul Huza’i Zakariyya Aliyu ya bayar da umarnin tsare matashin a gidan maza na tsawon shekara guda ko kuma zabin biyan tarar Naira dubu 30.