An daure shi shekara 14 saboda yi wa yarinya fyade

Babbar Kotun Jihar Kano ta Shida ta daure wani matashi mai shekara 35 tsawon shekara 14 a gidan kurkuku ba tare da zabin biyan tara ba, saboda samunsa da laifin yi wa wata yarinya fyade.Wanda ake zargin mai suna Jibrin Aminu ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 (an boye sunanta) fyade ne bayan […]

An daure shi shekara 14 saboda yi wa yarinya fyade

Babbar Kotun Jihar Kano ta Shida ta daure wani matashi mai shekara 35 tsawon shekara 14 a gidan kurkuku ba tare da zabin biyan tara ba, saboda samunsa da laifin yi wa wata yarinya fyade.
Wanda ake zargin mai suna Jibrin Aminu ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 (an boye sunanta) fyade ne bayan ya yaudare ta ya shigar da ita shagonsa.
dan sanda mai gabatar da kara Umar Sani ya bayyana wa kotun cewa laifin da ake zargin Jibrin Aminu ya saba wa sashi na 283 na kundin final kod na shekarar 2000.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda alkalin kotun Mai shari’a A’isha R. B. ta yanke masa hukuncin daurin shekara 14 ba tare da zabin biyan tara ba.
A wani labarin wata matar aure mai shekara 33 ta gurfanar da mijinta a gaban Kotun Musulunci ta Fagge Waje tana neman a raba aurensu domin tsira da ranta daga yunkurin da kanen mijin ke yi na halaka ta.
Matar mai suna A’isha Hamza da ke Unguwar Kwana Hudu a yankin Nassarawa ta shaida wa kotu cewa kimanin wata uku da suka gabata kanen mijin mai suna Inuwa Usman ya rika kiranta karuwa kuma ya ce zai kashe ta. “Wata rana ya zo gidanmu ya tambayi yayansa da na ce ba ya nan, sai ya fito da wuka ya rika daba min, sannan ya gudu. Makwabta ne suka kai ni asibiti aka yi min jinyar raunukan da ya yi min a kai da fuska da bayana,” inji ta.
A’isha ta ce tun daga lokacin wanda ake zargin ya buya, kuma mijinta bai yi wani kokari don nemansa ba, balle ya fuskanci hukunci, don haka take neman saki daga mijin.
Da kotun ta waiwayi mijin mai suna dahiru Usman ya ce, ba kamar yadda ta fadi ba, ya yi kokarin nemo dan uwansa amma bai same shi ba, kuma ya roki kotun ta ba shi biko.
Alkalin kotun Mai shari’a Abubakar M. Ayagi ya ba shi biko don yin sulhu da matarsa, kuma ya nemi mijin ya zo da kanensa a zaman kotun na gaba.