An daure shi shekara 7 saboda ‘rashin saurin intanet’

Mutumin da ya kona kayan samar wa gwamnati saboda rashin saurin intanet

An daure shi shekara 7 saboda ‘rashin saurin intanet’

Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari saboda ya kona kayan sadarwar intanet a kasar China.

Mutumin ya cinna wa wayoyin sadarwar intanet din wuta ne a wani shagon intanet a lardin Guangxi, bayan ya fusata saboda rashin saurin intanet a lokacin da yake amfani da shi.

Kotun ta ce sai da mutumin ya cinna wa wani tsumma da ke hannunsa wuta sannan ya yi amfani da tsummar wajen kona kayan sadarwar intanet din gwamnati.

Ta bayyana cewa abin da ya aikata din a watan Yunin 2021 ya yi sanadiyyar katsewar intanet a gidaje da ofisoshi 4,000 na tsawon awa 28 zuwa 50, ciki har da wani asibitin gwamnati.

“Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kwace abin da mutumin ya yi amfani da shi a wajen tayar da wutar,” inji kotun da ke zamanta a wani karamin gari mai suna Cenxi.

Daga baya ne alkali ya yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari saboda “laifin lalata kayan sadarwar intanet mallakin gwamanti.