An daure sojojin Kenya kan kwasar ganima lokacin harin Westgate

Sojojin kasar Kenya biyu sun rasa kakinsu kuma an daure su sakamakon samunsu da laifin kwasar ganima a lokacin da aka kai hari kantin Westgate a watan jiya.Shugaban Sojan kasar Janar Julius Karangi ne ya bayyana haka, inda ya ce ana ci gaba da bincike kan soja na uku. Sai dai ya musanta zargin cewa […]

An daure sojojin Kenya kan kwasar ganima lokacin harin Westgate

Sojojin kasar Kenya biyu sun rasa kakinsu kuma an daure su sakamakon samunsu da laifin kwasar ganima a lokacin da aka kai hari kantin Westgate a watan jiya.
Shugaban Sojan kasar Janar Julius Karangi ne ya bayyana haka, inda ya ce ana ci gaba da bincike kan soja na uku. Sai dai ya musanta zargin cewa ‘an tafka gagarumar kwasar ganima,” inda ya ce kafafen watsa labarai ne kawai ke yunkurin shafa wa sojojin kashin kaji don nuna “ba su da kwarewa.”
kungiyar Al-Shabbab ta kasar Somaliya ta dauki nauyin kai harin da ya ci rayukan mutum 67 a cikin yini hudu.
Wata kyamarar CCTb da kafafen watsa labarai na kasar suka fitar ta nuna sojojin suna kwasar kaya a katin na Westgate lokacin artabu.
Janar Karangi a baya ya ce sojojin sun dauki ruwa ne kawai saboda suna jin kishi, amma a ranar Talatar da ta gabata, ya ce sn kori sojoji biyu bayan an same su da kayayyakin da suka hada da wayoyin hannu da kyamarori da suka sace daga kantin.
Kakakin sojojin kasar Kanar Cyrus Oguna ya ce wani karamin kwamanda ne ya ba sojojin umarnin su dauki abinci a kantin. Kuma Janar Karangi ya ce wannan kuskure ne daga kwamandan da suke kokarin gyarawa.
Masu shaguna da ke harabar rukunin kanunan sun ce an sace musu kayayaki a yayin artabun.