An daure su shekara shida kan shiga gidan ’yarsu

Kotu ta yanke hukuncin ɗaurin shida ga wani magidanci da matarsa da ’ya’yansu biyar kan shiga gidan surukinsu.

An daure su shekara shida kan shiga gidan ’yarsu

Kurkuku

Kotu ta yanke hukuncin ɗaurin shida ga wani magidanci da matarsa da ’ya’yansu biyar kan shiga gidan surukinsu.

Kotun Majisatare da ke Ilori a Jihar Kwara ta yanke wa ma’auratan hukuncin ne bayan mijin ’yarsu ya yi karar su bisa zargin su da hada baki da aikata laifi da fasa gida da kuma razana jama’a da sata.

Mai karan, Ajayi Oluwafemi, ya zargi surukan nasa da kutse a gidansa da sace masa kudade da wasu kadarori, sakamakon sabanin da aka samu tsakaninsa da matarsa.

Ya shaida wa ’yan sanda cewa surukan nasa sun yi kutse a gidansa inda suka kai masa hari, suka yi awon gaba da tsabar kudinsa Naira miliyan 1.2 da talabijin na bango da sauran kayayyaki da sunan kwashe kayan ’yarsu daga gidan.

Ya ci gaba da cewa surukan nasa sun sha kai masa hari a gidansa, kuma sun taba daukar hayar ’yan daba suka dauke shi suka kai shi daji, kafin daga bisani a ceto shi.

Tun shekarar 2021 ake wannan shari’a kafin alkalin kotun Kudirat Yahaya, ta yanke hukuncin daurin shekara shida-shida ga Mista Adedokun Paul da matarsa da ’ya’yansu biyar da ake kara.

Mai Shari’a Kudirat Yahaya ta ce kotu ta samu wadanda aka gurfanar din da duk laifuka biyar da ake tuhumar su da aikatawa, wanda ke iya haddasa rashin zaman lafiya a cikin al’umma.

Sai dai kuma kotun ta sallami wanda ake kara na bakwai, kasancewarsa karamin yaro ne a lokacin da ya ba da shaida kan abin da ya faru.

Amma kotun ta ba wa wadanda aka yanke wa hukuncin zabin biyan tarar Naira 25,000 ga kowannensu, ko kuma zaman gidana yari.

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso