An daure tantabara don laifin leken asiri a Indiya
A karshen makon jiya ne ’yan sanda a kasar Indiya suka daure wata tantabara saboda zargin da yi wa makwabciyarta wato kasar Pakistan aikin leken asiri. An kama tantabarar ce bayan an ganta tana dauke da wata na’ura da wasu sakonni da aka rubuta da harshen Urdu (harshen kasar Pakistan) da kuma lambar rundunar ’yan […]
A karshen makon jiya ne ’yan sanda a kasar Indiya suka daure wata tantabara saboda zargin da yi wa makwabciyarta wato kasar Pakistan aikin leken asiri.
An kama tantabarar ce bayan an ganta tana dauke da wata na’ura da wasu sakonni da aka rubuta da harshen Urdu (harshen kasar Pakistan) da kuma lambar rundunar ’yan sandan kasar Pakistan.
Tantabarar ta shiga hannu ne a wani kauye da ke iyakar kasar Indiya da Pakistan, inda wani yaro mai kimanin shekara 14 ya kama tantabarar kafin daga bisani ya mika wa ofis ’yan sanda da ke kusa.
kasashen Indiya da Pakistan kasahe biyu wadanda ba sag a maciji da juna. Hakan ya sa suka sha fafata yaki a tsakaninsu. Kuma idan ba a manta ba kasar Pakistan ta balle ne daga Indiya a shekarar 1947.