An daure tsoho shekara 7 kan luwadi

Babbar Kotun Majistare ta daya da ke Dutse a karkashin jagorancin Mai shari’a Sadam Habibu ta daure wabi tsoho mai shekara 75, shekara bakwai a gidan maza saboda samunsa da kotun ta yi da aikata luwadi da wani yaro dan shekara takwas. Tsohon mai suna Adamu Aliyu Marma da ke zaune a kauyan Karma cikin […]

An daure tsoho shekara 7 kan luwadi

Babbar Kotun Majistare ta daya da ke Dutse a karkashin jagorancin Mai shari’a Sadam Habibu ta daure wabi tsoho mai shekara 75, shekara bakwai a gidan maza saboda samunsa da kotun ta yi da aikata luwadi da wani yaro dan shekara takwas.

Tsohon mai suna Adamu Aliyu Marma da ke zaune a kauyan Karma cikin karamar Hukumar Guru ya amsa laifinsa, sai dai ya ce yaron mai suna Adamu (an sakaya cikakken sunansa) ya same shi a wani kango ya ce masa ya yi luwadi da shi ya ba shi wasu ’yan kudi saboda yana da wata matsala da ta dame shi da yake son magancewa

Ya ce saboda haka ya ba shi kudin kuma ya aikata luwadin da yaron. Tsohon ya ce bokansa ne ya ce masa idan ya yi luwadi da kananan yara zai zama miloniya kuma zai shahara a yankin na Marma wajen mallakar abin duniya.

Tsohon ya kara da cewa bayanin da bokan nasa ya yi masa ne ya sa shi aikata laifin.

Sakamakon ikirarin da tsohon ya yi ne kotun ta yanke masa hukunci bisa dogaro da amsa laifinsa ta daure shi shekaru bakwai ba beli ko zabin biyan tara.