An daure tsohon Fira Ministan Pakistan Imran Khan shekara 14 kan rashawa

Kotu ta yanke wa tsohon Fira Ministan Pakistan, Imran Khan, hukuncin daurin shekara 14 kan laifin cin hanci da rashawa.

An daure tsohon Fira Ministan Pakistan Imran Khan shekara 14 kan rashawa

Kotu ta yanke wa tsohon Fira Ministan Pakistan, Imran Khan, hukuncin daurin shekara 14 kan laifin cin hanci da rashawa.

A ranar Juma’a kotun ta yanke masa hukunci tare da matarsa, Bushra Bibi, kan laifin da ke alaka da binciken safarar kudaden haram da aka yi masa a kasar Birtaniya.

Alkalin kotun, Nasir Javed Rana, ya ce duk da cewa Imran Khan na zaman kaso kan laifin rashawa, an kara samun sa da laifukan da kuma amfani da kujerarsa da fira minista ta haramtacciyar hanya.

Mai gabatar da kara, Muzaffar Abbasi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an yanke wa matar Imran Khan wadda ake tuhumar su tare hukuncin daurin shekara bakwai, saboda laifin taimaka masa wajen aikata laifin.

Lauyan Mista Khan, Faisal Chaudhry ya ce za su daukaka kara, yana mai zargin adawar siyasa ce ta sa aka yanke masa awnnan hukunci.

An yanke wa Khan da matsarsa hukuncin ne kan zargin mayar da Dala miliyan 231 ga mai harkar gidaje dan kasar Pakistan bayan hukumar binciken laifuka ta kasar Birtaniya ta gano kudaden, das ake zargin safarar su ya yi ba bisa ka’ida ba.

Ya kamata a mayar da kudaden ne ga asusun gwamantin Pakistan, kuma ana zargin dan kasuwan ya ba wa Mista Khan da matarsa wasu gidade ta hannun wata kungiyar jinkai da suka kafa, saboda dawo masa da kudaden da suka yi .

Khan shi ne fira ministan Pakistan daga 2018 zuwa 2022 lokacin da aka tsige shi bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da sojojin kasar da ke juya akalar gwamnati.

A halin yanzu dai ya haura shekara guda tun watan Agustan 2023, a gidan yari a matsayin fursuna bayan samun sa da laifin rashawa.