An daure wadanda suka zargi wata da maita wata uku-uku
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse ta yanke hukuncin daurin wata uku-uku ga wasu mutane da suka bata wa wata mace suna ta yi mata kazafin ita mayya ce tare da neman hallaka ta. Matar mata mai suna Maryam Jidawa ta shigar da karar mutanen ne su bakwai a gaban kotu, inda ta ce ba […]
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse ta yanke hukuncin daurin wata uku-uku ga wasu mutane da suka bata wa wata mace suna ta yi mata kazafin ita mayya ce tare da neman hallaka ta.
Matar mata mai suna Maryam Jidawa ta shigar da karar mutanen ne su bakwai a gaban kotu, inda ta ce ba domin Mai unguwar Jidawa ba da tuni mutanen sun kashe ta, domin sun je gidanta dauke da gorori da sanduna suna neman hallaka ta.
Da Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Jibrin Ibrahim ya waiwayi wadanda ake tuhumar uku daga ciki sun amsa cewa sun zarge ta da maita, amma sun musanta laifin daukar makami da kokarin hallaka ta, wadanda suka amsa laifin su ne Salamatu Ibrahim da Ado Gero da kuma Jafaru Sa’adu, yayin da mutum hudu wato Bayero Sa’adu da Tataru Ya’u da Bala Ya’u da Hamidu Ya’u suka ce ba su aikata laifin da matar ta yi kararsu a kai ba.
Kotun ta yi wa wadanda suka amsa laifinsu hukunci biyan tarar Naira 2000 kowannesu kuma za su bai wa matar Naira dubu biyar-biyar a matsayin kudin bata mata suna ko su tafi kurkuku na wata uku-uku.
Su kuwa mutum hudu da suka musanta zargin, kotun ta mika su ga ’yan sanda su ci gaba da bincike zuwa lokacin da za a sake gabatar da su a gaban kotu.