An daure wanda ya karya hannun mahaifinsa wata shida
Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge da Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Shu’aibu Musa hukuncin daurin wata shida ba tare da zabin biyan tara ba saboda samunsa da laifin karya hannun mahaifinsa.Matashin mai shekara 29 kuma mazaunin unguwar Kawo a birnin Kano kimanin wata biyu da suka ya yi wa mahaifinsa mai […]

Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge da Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Shu’aibu Musa hukuncin daurin wata shida ba tare da zabin biyan tara ba saboda samunsa da laifin karya hannun mahaifinsa.
Matashin mai shekara 29 kuma mazaunin unguwar Kawo a birnin Kano kimanin wata biyu da suka ya yi wa mahaifinsa mai suna Musa Shua’aibu duka har ya karya masa hannu.
Mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa a lokacin da aka kama Shu’aibu an same shi da kwalabe masu dauke da abubuwan sa maye.
Wanda ake zargin ya amsa laifuffukan da ake zarginsa na jawo rauni da kuma samunsa da abubuwan maye, laifuffukan da suka saba wa sashi na 159 da 165 na kundin shari’ar na Jihar Kano.
Shu’aibu ya shaida wa kotun cewa mahaifinsa ya dibar masa kudinsa ne inda a dalilin neman kudin ne ya karya masa hannu.
Alkalin kotun Abdu Abdullahi Waiya ya yanke wa mai laifin daurin watani shida ba tare da zabin biyan tara ba, kuma ya yanke masa hukuncin daurin wata shida ko biyan tarar Naira dubu 10, kan laifi na biyu.
A wani labarin kuma Kotun Shari’ar Musulunci da ke ’Yan alluna a Fagge ta daure wani matashi mai kimanin shekara 26 mai suna Zaharaddin dahiru saboda samunsa da laifin yin lalata da matar aure a unguwar Kurna a karamar Hukumar Dala, Jihar Kano.
Zaharaddin dahiru da abokiyar lalatarsa Daraja Abdullahi asirinsu ya tonu ne a yayin da mijin Darajar mai suna Auwalu Zubairu ya kama su a cikin dakin matarsa a lokacin da ya dawo daga wurin sana’arsa.
Laifin da ya saba wa sashi na 164 na kundin shari’ar Musulunci na Jihar Kano na shekarar 2000.
Wanda ake zargin na farko ya shaida wa kotu cewa a duk lokacin da mijin Daraja wanda direban tasi ne ya fita wurin aikinsa sai matar tasa ta gayyace shi gidanta don ya biya mata bukata.
Alkalin kotun Abubakar Ayagi daure Zaharaddin dahiru shekara daya ko ya biya tarar Naira dubu 20, da kuma daurin wata daya ba tare da zabin tara ba da kuma bulala 20.
Ita ma Daraja Abdullahi, Alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata shida ko biyan tarar Naira dubu 10.