An daure wanda ya yi wa tsohuwar budurwarsa waya sau dubu da 807 a Faransa

Wani mutumi dan kasar Faransa, dan shekara 33, ya shiga gidan kason, bayan da ya kira wayar tsohuwar budurwarsa, tare da aike mta da sakonnin tes, har dubu da 807.Wannan mai laifi da ba a bayyana sunansa ba, wai ya bukaci tsohuwar budurwar tasa ne, ta yi masa godiya kan gyaran da ya yi musu […]

An daure wanda ya yi wa tsohuwar budurwarsa waya sau dubu da 807 a Faransa
An daure wanda ya yi wa tsohuwar budurwarsa waya sau dubu da 807 a Faransa

Wani mutumi dan kasar Faransa, dan shekara 33, ya shiga gidan kason, bayan da ya kira wayar tsohuwar budurwarsa, tare da aike mta da sakonnin tes, har dubu da 807.
Wannan mai laifi da ba a bayyana sunansa ba, wai ya bukaci tsohuwar budurwar tasa ne, ta yi masa godiya kan gyaran da ya yi musu a gida.
Wanda ake tuhuma da aikata wannan laifi, tuni aka yanke masa hukuncin zaman kurkuku na tsawon wata 10, amma an zaftare wata shida, sannan zai biya tarar kudin Yuro dubu guda.
Mutumin da ake tuhuma da aikata wannan laifi, ya bukaci a biyashi ludin aikin da ya yi a gidan su yarinyar.
“A lokacin na nufin tursasata ta biya ni ladar aiki, ko kuma a kalla ta ce da ni ‘na gode.’ Don haka  na ki daina kiranta,” inji shi.
Mai laifin ya sanar da kotu a garin Lyon cewa, ya dakatar da kiran ne bayan da wani mutum ya shiga tsakaninsu, inda aka matsa amta ta ce, ‘na gode maka,’ sannan na daina matsa a mata da kira. Tun daga wancan lokacin bai sake kiranta ba, kamar yadda Kamfnain Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.