An daure wani saboda ya auri uwa da ’yarta a lokaci guda
Wani mutum dan asalin Pennsylvania mai suna Christopher Hauftmann yanzu haka an tura shi gidan yari saboda yadda wata kotu a kasar ta same shi da laifin auren wata mata tare da ’yarta a lokaci guda. Mutumin mai shekara 44, ya auri matar ce mai shekara 43 da kuma ’yarta mai shekara 18 a lokaci […]

Wani mutum dan asalin Pennsylvania mai suna Christopher Hauftmann yanzu haka an tura shi gidan yari saboda yadda wata kotu a kasar ta same shi da laifin auren wata mata tare da ’yarta a lokaci guda.
Mutumin mai shekara 44, ya auri matar ce mai shekara 43 da kuma ’yarta mai shekara 18 a lokaci guda ba tare da ya rabu da uwar yarinyar ba. Hakan ya saba wa dokar kasar da hakan ta sa aka tasa keyarsa zuwa gidan yari