An daure wasu ’yan jarida uku a Masar kan hira da ’yan Ikhwanu
Hukumomin Masar sun yanke hukuncin daurin kwana 15 ga wasu manema labaru su uku da ke aiki da gidan talabijin na Al-Jazeera.Wakiliyar BBC ta ce, wata sanarwa daga ofishin mai gabatar da dara na dasar Masar ta ce ana zargin manema labaran ne da shiga wata dungiyar ’yan ta’adda da aka haramta, kuma suna ba […]
Hukumomin Masar sun yanke hukuncin daurin kwana 15 ga wasu manema labaru su uku da ke aiki da gidan talabijin na Al-Jazeera.
Wakiliyar BBC ta ce, wata sanarwa daga ofishin mai gabatar da dara na dasar Masar ta ce ana zargin manema labaran ne da shiga wata dungiyar ’yan ta’adda da aka haramta, kuma suna ba da labaran darya da ke zubar da dimar dasar Masar.
Mutanen uku sun hada da tsohon wakilin BBC, Peter Greste, wanda dan dasar Ostireliya ne.
Sai dai mahukuntan Masar din sun sako wani mai daukar hoto da aka kama tare da manema labaran uku.
A ranar Talata ce Ministan Harkokin Cikin Gidan dasar ya bayyana kama ’yan jaridar inda ya ce sun tattauna da mambobin dungiyar Ikhwanul Muslimina ba bisa da’ida ba, bayan mahukuntar dasar sun ayyana ta a matsayin dungiyar ’yan ta’adda a makon jiya.
Ya dara da cewa Al-Jazeera na watsa labaran da suke barazana ga tsaron dasar, an kuma dwace kayan aikin ’yan jaridar da suka hada da na’urar daukar hoto da ta nadar magana.
Sojoji sun hambarar da gwamnatin Mohammad Morsi dan dungiyar Ikhwanu a watan Yulin bara, sannan Gwamnatin ridon dwarya da ke samun goyon bayan sojoji a Masar ta ayyana dungiyar a matsayin ta ’yan ta’adda, matakin dai zai ba gwamnatin damar dwace kadarorin dungiyar.
Mahukuntan dasar sun zargi dungiyar da kai hari kan hedkwatar ’yan sanda a ranar Talatar makon jiya a birnin Mansoura da ke Arewacin dasar.