An daure wata mata saboda bincikar wayar mijinta
Wata kotu ta yanke wa wata mata hukuncin daurin wata uku saboda bincikar wayar mijinta ba tare da izininsa ba. Mijin matar ya shigar da karar uwargidansa ne bisa binciken sirri da take yi a wayar hannusa. Kotun Ras Al Khaimah da ke Arewacin Hadaddiyar Daular Larabawa ta yanke wa matar hukunci ne bisa samunta […]
Wata kotu ta yanke wa wata mata hukuncin daurin wata uku saboda bincikar wayar mijinta ba tare da izininsa ba.
Mijin matar ya shigar da karar uwargidansa ne bisa binciken sirri da take yi a wayar hannusa.
Kotun Ras Al Khaimah da ke Arewacin Hadaddiyar Daular Larabawa ta yanke wa matar hukunci ne bisa samunta da laifi.
A jawabin mijin ya ce, matarsa ta kasance tana bincikar wayarsa tare da kwafe duk wasu bayanan sirri da ke cikin wayar har zuwa ranar da ya shigar da karar.
Maigidan ya yi korafin abin da matarsa ke yi masa na bincikar bayanan wayarsa lokacin da yake barci. Matar ta tura wasu hotuna da wasu bayanan muhawara zuwa wayarta don sanin sirrin wayarsa.
Sai dai matar ta bayyana wa kotun cewa, mijinta ya ba ta kalmar sirrin ta bude wayarsa tun lokacin da ta kama shi yana hulda da wadansu mata a shafukan sadarwa a wayarsa a kwanaki baya.
Kasar Daular Larabawan dai ta sanya dokoki masu karfi game da tsaron bayanan sirrin dan Adam a shafukan intanet.