An daure wata mata saboda wulakanta dan sanda
A yau kotun Karmo ‘Grade 1 Area Court’ da ke Abuja ta daure wata mata Faith Kathy na wata biyu a gidan yari saboda wulakanta jami’in dan sandan Najeriya da gangan. Alkalin kotun Inuwa Maiwada ne zartar da hukuncin tare da cin tarar naira 3,000 kuma ya bukace ta da ta zama mai dabi’a ta […]
A yau kotun Karmo ‘Grade 1 Area Court’ da ke Abuja ta daure wata mata Faith Kathy na wata biyu a gidan yari saboda wulakanta jami’in dan sandan Najeriya da gangan.
Alkalin kotun Inuwa Maiwada ne zartar da hukuncin tare da cin tarar naira 3,000 kuma ya bukace ta da ta zama mai dabi’a ta gari.
Kathy, na zaune ne a yankin Utako dake Abuja. Jami’in dan sandan Ijeoma Ukagha na ofishin ‘yan sanda na yankin Utako ne ya shigar da karar.