An daure ’yan Boko Haram shekara 75

Wata babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wasu ’yan kungiyar Boko Haram uku hukuncin daurin shekara 75 da aiki mai tsanani.Mutum ukun da kotu ta samu da laifi, kowannensu zai shafe shekara 25 a gidan yari saboda shiga kungiyar ta’addanci.An gudanar da wannan shari’ar ce cikin sirri inda aka hana manema labarai […]

An daure ’yan Boko Haram shekara 75
An daure ’yan Boko Haram shekara 75

Wata babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wasu ’yan kungiyar Boko Haram uku hukuncin daurin shekara 75 da aiki mai tsanani.
Mutum ukun da kotu ta samu da laifi, kowannensu zai shafe shekara 25 a gidan yari saboda shiga kungiyar ta’addanci.
An gudanar da wannan shari’ar ce cikin sirri inda aka hana manema labarai halarta a wani yunkuri na kare rayukan masu ba da shaida.
Tunda farko alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Buba, ya bukaci ra’ayin lauyoyin masu gabatar da kara da na kariya kan halaccin yin shari’ar a cikin sirri, bayan da Babban Lauyan Jihar Legas Ade Ipaye da mai gabatar da kara suka bukaci haka a watan Disamban bara.
A ranar Talata Mista Ipaye ya sake nanata matsayinsa, inda ya ce tunda an yi zaman shari’ar cikin sirri, ya wajaba a yanke hukunci cikin sirri, kuma lauyan kariya ya amince da bukatar. Don haka alkalin ya bukaci manema labarai da ’yan kallo su fice daga cikin kotun.
An gabatar da mutum 17 ne da ake zargi da laifuffuka takwas da suka hada da ta’addanci da mallakar makamai da kasancewa ’ya’yan haramtacciyar kungiya, sai dai mutum hudu da suka hada da Ali Mohammed da Adamu Karumi da Ibrahim Usman da Bala Haruna, Idris Ali ne aka yanke wa hukunci, inda aka daure ukun farko aka sallami Idris Ali, saboda rashin hujja kan zargin da ake yi masa.
An kama wadanda aka yanke musu hukuncin ne a ranar 21 ga Maris din bara a gini mai lamba 5, Road 69, Lekki Phase I Housing Estate da mai Lamba 24, Oyegbeni St., Ijora-Oloye, Apapa-Iganmu, Legas dauke da fakitin hada bama-bamai uku da bama-bamai 15 da bindigogi kirar AK47 guda 11 da harsasai 30 da sauransu.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi