An dawo da dokar kulle a jihar Osun
An sake kakaba dokar kulle a kananan hukumomi hudu sakamakon saurin yaduwar cutar coronavirus a jihar Osun. Dokar kullen ta mako guda ta shafi kananan hukumomin Ilesa ta Gabas da Ilesa ta Yamma da Atakumosa ta Gabas da kuma Atakumosa ta Yamma, daga ranar Talata bakwai ga watan Yuli. ‘Za a sake dawo da dokar […]
An sake kakaba dokar kulle a kananan hukumomi hudu sakamakon saurin yaduwar cutar coronavirus a jihar Osun.
Dokar kullen ta mako guda ta shafi kananan hukumomin Ilesa ta Gabas da Ilesa ta Yamma da Atakumosa ta Gabas da kuma Atakumosa ta Yamma, daga ranar Talata bakwai ga watan Yuli.
- ‘Za a sake dawo da dokar kulle a Osun’
- Wasu masu coronavirus a Osun sun tsere bayan killace su
- Almajirai 193 sun kamu da coronavirus a Kano
Kwamishinar yada labaran jihar, Funke Egbemode, ta ce, “Za a rufe dukkanin manyan kasuwanni a kananan hukumomin hudu, face shagunan cikin unguwa da wuraren sayar da magunguna”.
Don haka ta bukaci jama’a su yi amfani da kwanakin da suka rage su tanadi kayan bukatunsu, kuma su rika kiyaye ka’idojin dokar kullen domin guje wa fushin hukuma.
Kwamishinar ta ce umarnin na Gwamna Gboyega Oyetola ya biyo bayan ganawar gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin hudu.
Ta ce yanayin yadda al’umman yankunan ke kiyaye dokar ne zai ba da damar sassautawa ko tsawaita ta bayan mako guda da aka diba a karon farko.
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta kara tsawaita sassaucin da ta yi a sauran kananan hukumomin jihar da mako biyu.
Sai dai za ta rika da lura da yanayin karuwar alkaluman cutar a sauran yankunan domin daukar matakin da ya dace.